Tabarbarewar Tarbiyya: Daga Ina Matsalar Take? – Jiddah Gaya

402

Tarbiyya kalma ce da ta samo asali daga Harshen Larabci. Tarbiyya wani bangare ne ko jigo a rayuwar Dan Adam. Manufar Tarbiyya shine, gina mutum ya tashi cikin kyawawan halaye da dabi’u.


Tarbiyya a Hausa na nufin, cikakken Mutum wanda yake da halaye da dabi’u masu inganci. Akan alakanta mutum mai nutsuwa, mai girmama na gaba, mai sanin yakamata, mai iya kalami, mai kyakkyawar mu’amula da suna mai Tarbiyya. A takaice, mutum na samun cikakkiyar daraja da mutumtaka a idon jama’a idan ya kasance mai Tarbiyya.


Jigon masu bada tarbiyya ga Dan Adam sune; Iyaye da Al’umma. Yayin da a bangare guda ake alakanta masu bata tarbiya da; Baragurbin abokai da kuma Kwaikwayo daga abubuwan da ake kalla na yau da kullum wanda daga bisani sai mutum ya fara kwaikwayon ko aiwatar da abinda yake kalla, kamar daga fina finai, wakoki, raye raye da sauransu.


Manazarta sun zayyana hanyoyi/ matakan bada tarbiyya kamar haka; Nuni, Lura ko Kula, Umarni da kuma Hani ko Kwaba.


Tabarbarewar tarbiyya, wani babban kalubale ne da ake kokawa akansa a halin yanzu. Al’amarin yayi tsamarin da iyaye da kansu na kokawa kan lalacewar tarbiyyar ya’yan’ da suka haifa. To ko ina gizo ke sakar?


Da dama na alakanta hakan da sakacin iyaye wajen dabbaka wadancan matakai guda hudu wato; Nuni, Lura/Kula, Umarni, Hani/Kwaba.


A hannu guda kuma, wasu na alakanta tabarbarewar tarbiyya da wanzuwar bakin al’adu da cudanya da mutane masu karancin tarbiyya.


Yayin da wani bangaren ke alakanta hakan da yawaitar tashoshin talabijin da wayoyin hannu wanda ke dauke da manhajoji da shafuka iri iri wanda sukan taka muhimmiyar rawa wajen taba tarbiyya.


Dukka wadannan na samun wajene suyi tasiri wajen gurbata tarbiyyar yaro idan iyaye sukayi sakaci wajen bibiyar yadda ‘yayan’ su ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.


Akwai bukatar iyaye su zage damtse wajen dawo da tarbiyya yara kan hanya, ta hanyar; Nuna musu abinda yake dai dai da sabanin haka, ka kuma kasance madubin da yaranka zasuyi kwaikwayo daga gare ka, da Lura akan wadan da suke mu’amula dasu da bibiyar al’amuran da suke gudanarwa da wayoyinsu na hannu kasancewar kaso mai yawa na abubuwan rashin gaskiya na faruwa ne ta hanyar amfani da wayar hannu, na karshe kwabarsu kan wani abu da suke ba dai dai ba.


Hauwa Shu’aibu Gaya, Yar Jarida Ce Kuma Mai Yin Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Ta Rubuto Daga Birnin Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan