Yadda Bindigar Shaida Ta Harbe Lauya A Kotu

309

‘Yan sanda a Afirka ta Kudu sun ce wata lauya ta gamu da ajalinta, a lokacin da harsashi ya kufce bisa kuskure daga bindigar da aka kawo kotu dan kafa shaida da ita a yankin KwaZulu Natal.

Lauyar mai suna Adelaide Ferreira-Watt ta gamu da ajalinta jim kadan bayan harbin da bindigar ta yi ma ta a kwankwasonta.

Kunamar bindigar ta dana kanta a dai-dai lokacin da aka gabatar da ita a matsayin shaida gaban alkali kan fashi da makami da aka yi a wani gida,

‘Yan sanda sun ce su na gudanar da bincike kan mutuwar Miss Ferreira-Watt a matsayin kisa ba da gangan ba.

Za kuma su yi bincike kan dalilin da ya sa aka kawo bindigar kotu alhalin akwai harsashi a cikinta, dan hakan ya sabawa ka’ida.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan