A Karon Farko An Samar Da Katafareren Shagon Sayar Da Tabar Wiwi

320

A karon farko a tarihin birnin Trinidad da ke jihar Colorado da ke kasar Amurka, an samar da wani katafareren shagon sayar da tabar wiwi.

Tun da farko wadanda su ka samar da wannan shago Deve Chris Elkins da Sean Sheridan sun bayyana cewa birnin Trinidad shi ne birnin da ya dace da wannan shago, musamman idan aka yi la’akari da dokoin birnin.

Hukumomin a birnin na hasashen sayar da tabar zai habbaka hanyoyin samar da haraji ga gwamnati da akalla dalar Amurka Miliyan 67 a kowace shekara tare da samar da ayyukan yi da karuwar yawan baki masu yawon bude ido a Jihar.

Sai dai masu karbar haraji sun zura ido domin ganin yadda harkar cinikayyar tabar za ta habbaka tattalin arziki sakamakon halatta yin amfani da ita a karkashin doka.


Akalla jahohin Amurka 19 ne ke da damar yin amfani da ganyen tabar wiwi domin yin magani, yayin da amincewa da wannan mataki a hukumance ke bai wa al’ummar Jihohin kasar damar shan wannan ganye a wuraren shakatawa ba tare da fuskantar fushin hukuma ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan