Al’ummar Masarautun Rano Da Karaye Sun Yi Zanga-zangar Lumana

342

Al’ummar masarautun Rano da Karaye sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, sakamakon hukuncin kotun mai shari’a Usman Na’abba da ta soke dokar da ta bayar da damar yin masarautu a jihar Kano.

Tun da farko dai daruruwan maza da mata ne su ka fito kan tituna dauke da kwalaye mai dauke da nuna goyon bayan Sarakunan tare kuma da yin Allah wadai da wannan hukunci.


A masarautar Rano, zanga-zangar lumanar ta samu jagorancin shugaban karamar hukumar Honrabul Abdullahi Ya’u Gidan Zangi.


A karshe masu zanga-zangar sun karkare a fadar mai martaba Sarkin Rano, Alh. (Dr) Tafida Abubakar Ila, in da aka yi addu’ar Allah ya tabbatar da wannan masarauta, domin cigaban al’ummar wannan yanki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan