Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Ƙananan Hukumomi Sun Raba Biliyan N702 A Oktoba

52

A ranar Laraba ne Kwamitin Rabon Arziƙin Ƙasa, FAAC, ya raba jimillar kuɗi biliyan N702.058 ga matakan gwamnati uku na watan Oktoba.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris ya karanta bayan kammala taron na FAAC a Abuja.

Mista Idris ya ce biliyan N702.058 ɗin ya haɗa da kuɗin shiga da aka samu daga Harajin Kayayyaki wato VAT, ‘Exchange Gain’ da ‘Gross Statutory Revenue’.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N295.7, jihohi sun samu biliyan N192.697, ƙananan hukumomi kuma sun samu biliyan N144.9.

Ya ƙara da cewa jihohi masu samar da man fetur sun samu biliyan N49.1 a matsayin kuɗin shiga na jihohin dake samar da man fetur, Hukumomin Tattara Kuɗaɗen Shiga kuma sun samu biliyan N19.472 a matsayin kuɗin tattara kuɗaɗen shiga.

Mista Idris ya ce kuɗin shiga na ‘Gross Statutory Revenue’ a watan Oktoba sun kai biliyan N596.041.

A ta bakinsa, wannan adadi ya yi ƙasa da biliyan N3.660 idan aka kwatanta da biliyan N599.701 da aka samu a watan da ya gabata.

Ya ce kuɗaɗen shiga daga VAT ya ƙaru ya kai biliyan N104.910, maimakon biliyan N92.874 da aka raba a watan da ya gabata, an samu ƙarin biliyan N12.036.

A ta bakinsa, ‘Exchange Gain’ ya haifar da samun kuɗin shiga biliyan N1.107.

Ya ce zuwa 20 ga Nuwamba, ragowar kuɗin da yake a Asusun Rarar Kuɗaɗen Man Fetur dala miliyan 324 ne.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N15.107 daga VAT, jihohi sun samu biliyan N50.357, ƙananan hukumomi sun samu biliyan N35.250, inda Hukumomin Tattara Kuɗaɗen Shiga suka samu biliyan N4.196.

Ya ce a watan Oktoba, kuɗaɗen shiga daga Harajin Kuɗin Shigar Kamfanoni, CIT, VAT da kuɗaɗen da ake biya wa kaya da aka shigo da su daga waje sun ƙaru sosai, yayinda ‘Royaltie’, Harajin Ribar Man Fetur, PPT da ‘Excise’ Duty suka ragu sosai.

Mista Idris ya ce kwamitin ya ji daɗi da samun ƙarin kuɗin shigar da aka yi, ya kuma yi fatan hakan zai ɗore.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan