Babbar Kotun Tarayya ta Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’Abba, ta soke sabbin masarauutu huɗu da sabbin sarakuna da gwamnatin jihar Kano ta ƙirƙira.
A ranar 8 ga watan Mayu, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu a kan wata doka da ta jawo cece-ku-ce, wadda ta kafa ƙarin masarautu huɗu da sarakuna masu daraja ta ɗaya a Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya.
Majiyoyin cikin gida sun shida wa majiyarmu cewa gwamnan ne ya kawo dokar, amma sai aka fake da Majalisar Dokokin Jihar.
Da yake yanke hukuncin ranar Alhamis, kotun ta ce Majalisar Dokokin Jihar Kano ta saɓa wa tanadin Sashi na 101 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya ba majalisar dama ta ƙirƙiri dokoki.
Daga nan sai ya ce dokar da ta kafa sabbin masarautun ba ta da muhalli a shari’a.