Masu Murnar Rushe Masarautu Da Kotu Ta Yi, Murnar Banza Ku Ke – Salihu Tanko Yakasai

2042

Tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano akan kafafen sada zumunta, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa masu yin murna da hukuncin da kotu ta yi na rushe sababbin masarautu to hakika murnar banza su ke yi.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk, jim kadan da wata babbar kotu ta yi hukuncin rushe masarautun da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

“Masu murnar wai kotu ta soke sababbin masarautun mu na Bichi da Rano da Gaya da Karaye, wannan murnar ta ku ta wucin gadi ce, domin kuwa majalisa na da damar ta yi doka kuma an bi duk wata kai’da wajen yin dokar da ta haifar da masaraitun mu”

“Alkalii ya yi amfani da hujjar cewa wai bai kamata wani ya shigar da kuduri ba na yin doka sai dan majalisa, abin mamaki a wannan hujjar shi ne Kakakin Majalisa Majalisa wannan lokaci Hon Alhassan Rurum shi ne ya gabatar da kudurin bisa koke da wani ya kai wa majalisa”

“Domin haka akwai kuskure wajen wannan hujjar. Duk da haka dai, gwamnati za ta duba wannan hukunci kuma ta ga yadda zata tabbatar da zaman masarautun mu”


A karshe ya bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da jiran matakin da gwamnatin za ta dauka nan ba da jimawa ba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan