Sarkin Kano, Shi’a Da ‘Ya’YaN Sarki Ado Bayero : Martani Daga Farfesa Dahiru Yahaya

318

Da badon ba, ba zan yi martani ga takardar nan ta manema labarai da ‘ya’yan Sarki suka rubuta ba, saboda ba a kan ilimi suka ginata ba, a kan hamasa ce ta son kai. Amma sai na zabi in yi martanin, saboda haqqin da ke wuyana na bayyana gaskiya ga masu nemanta.

Na san Sarki Ado Bayero tun ina yaro, shi kuma yana sakandare. Babansa, Sarki Abdullahi Bayero ya alkinta haqqin kula da wannan yaro dan gata ga dan uwansa, mutumin Allah Galadiman Kano, Alhaji Muhammadu Inuwa, wanda shi ma ya zama Sarkin Kano na 12. Shi ma Galadiman Kano ya danqa haqqin kula da matashin dan Sarkin ga mahaifina wanda ya kasance sakatarensa ne, amininsa ne, kuma murshidinsa ne.

Mahaifina cikakken masani ne mai ra’ayin siyasar sauyi, wanda ya yi tasiri ga tunanin manyan masanan Kano na lokacinsa. Fuskokin irin su Aminu Kano, Isa Wali da Maitama Sule tamkar na Ado Bayero ne a gare ni domin na saba da su a gidan mahaifina tun ina dan qarami. Matar Ado Bayero ta farko ‘yar Galadiman Kano ce kuma a gidanmu ta taso. Ina cikin wadanda suka rakata gidan angonta a cikin birni daga Dawakin Kudu.

A lokacin da Galadima ya zama Sarki, na koma fada tare da shi. Saboda mahaifina ya rasu tun kafin nan, don haka sai na koma qarqashin kulawar Sarki. Na cigaba da zama a fada har zuwa lokacin da Ado Bayero ya gaji Alhaji Muhammadu Inuwa a matsayin Sarki. Na bar fada ne a lokacin da na gina gidana kuma na yi aure a shekarar 1967.

Na cika da mamaki a lokacin da marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim, ya ce wa wasu ma’aikatan fada da suka yi fushi cewa bai ji dadin wasu ra’ayoyina kan wasu ababe ba. Hakan ya nuna ina cikin muqarrabai uku na Sarkin Kano. Sauran su ne Shugaban Dariqar Qadiriyya, Sheikh Malam Nasiru Kabara, da Wazirin Kano, Marigayi Sheikh Malam Shehu Gidado. Na riqa rubuta wa Sarki takardun da yake gabatar wa a tarukan manyan mutane na duniya.

Babban abin da ya kyautata alaqar Ado Bayero da mahaifina shi ne qaunarsa da girmamawarsa ga mahaifin nawa. Mahaifina dan Shi’a ne wanda ya dauki Imam Ali a matsayin shugaba a bayan Annabi. Ya dauki Ahlulbaiti a matsayin mafita ga matsalar dan Adam. Kuma ya dauki Karbala a matsayin mafaka ga duk wanda aka zalunta.

Ba tare da shakka ba nake cewa, dukkan gidajen malaman da suka taimaka wa Sarakunan Kano ‘yan Shi’a ne. Mun yi bayanin yadda Sarki Abbas ya zamo dan Shi’a a wani rubutun daban. Don haka ma musun da Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi, ba’ada bayan rashin qimar musun a ilmance, to, kuma ba komai ba ne face maganar siyasa ta Sarki da ‘ya’yan Sarkin da ke cikin shakku. Qin magana ta ilimi ba dabi’ar gidan sarauta ba ne a ko’ina cikin fadin duniya. A lokacin da aka shaida wa Sarauniyar Ingila Elizabeth II a shekarar 1972 cewa tana cikin tsatson Annabi Muhammad (sawa), cewa ta yi ta ji dadi sosai. Sarauniyar tana girmama ilimi.

Na san Sarki Ado Bayero da mahaifinsa Sarki Abdullahi da surukinsa Sarki Muhammadu Inuwa suna da wasu halaye na Shi’a. Sarki Ado yana da yawan tawali’u, kuma mutum ne mai son tattaunawar ilimi. Yana da girmama manya daga bangarori daban-daban. Biyayyarsa ga mahaifiyarsa ba ta siffantuwa. Dabi’unsa na Shi’a suna da yawa. Yana da taimako ga talakawansa da ke cikin uqubar yunwa a boye. Yawancin malaman da ya fi girmamawa kuma yake hulda da suna da yanayin Shi’anci. Inkarinsa ga Izala sananne ne. Ya qi sallama mu su su yi wa’azi a Babban Masallacin Kano alhali ya yi wa ‘yan Shia lale marhabin. Da Sarki da ni, sam ba ma son Wahabiyanci kuma mukan yi magana a kan hakan. Ya bar matarsa wacce dalibata ce a jami’a cikin harkokin Shi’a.

A lokacin da aka gayyaci Wazirin Kano, Sheikh Malam Isa Waziri zuwa Iran don taya su murnar nasarar Juyin Juya Hali, sai ya nemi izini daga Sarki. Sai Sarki ya hana shi saboda taqiyyah. Inda kawai za ka gane Shiancin Sarki shi ne ta hanyar nazarin mutanen da suka kewaye shi. Dukkan Sarakunan da suka yi zamani bayan zuwan Turawan Ingila a kewaye suke da ‘yan Shi’a in banda Sarki Usman II wanda ‘yan gargajiya suka kewaye da kuma Sarki Muhammadu Sanusi I wanda ‘yan bokon da suka yi aiki da Turawa suka kewaye.

Mut’a, aure ne na wucin gadi wanda Allah ya yi maganarsa a Qur’ani a suratun Nisa’a aya ta 24. Manzon Allah ya halasta. Sahabbansa sun aikata. Asma’u ‘yar Sayyidina Abubakar ta yi auren mut’a da Ja’afar dan uwan Annabi. Sarki Ado Bayero, kamar mahaifinsa ne Sarki Abdullahi Bayero, kuma kamar wasu ne daga cikin Sahabbai, suna da matsananciyar sha’awa, kuma Allah ya samar da mut’ar nan don ta zama hanyar kwantar da wannan sha’awa ba tare da fadawa ga zinace-zinace ba.

Ina dai fatan cewa ‘ya’yan nan na Sarki ba so suke a kalli sananniyar rayuwar da mahaifinsu ya yi da mata a matsayin aikin zunubi ba tunda suna son haramta cewa mut’a ce ya yi. Allah ya tsare. Sarki Ado ya wuce duk yadda ‘ya’yansa suke tunani. Zina aba ce da Allah ya haramta a Qur’ani, wacce kuma ake ladabtarwa da kisa kamar yadda ya zo a ruwayoyi. Mut’a kuwa, rubutacciyar aba ce daga Allah, hastacciya daga Manzon Allah, aikatacciya ga Sahabbai.

Allah ya ce:

فَمَا اسْتَمْتَعْتُم بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً…

“Sa’annan abin da kuka ji dadi (mut’a) daga gare su (mata) to ku ba su sadakinsu wajibi ne…”

Asalin rubutun nan da Turanci Farfesa Dahiru Yahya ya yi. Ni na fassara ne. -MBI

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan