Ko Kaɗan Ba Na Tsoron Mutuwa- Obasanjo

271

Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olesegun Obasanjo, ya ce ba zai riƙa yin abubuwa kamar matsoraci saboda tsoron mutuwa, yana mai cewa, zai ci gaba da yin magana duk lokacin da ya ga abubuwa ba sa tafiya dai-dai a ƙasar.

Mista Obasanjo ya bayyana haka a wani taron Musayar Ra’ayi na Shirin Shirya Matasa na Shugaban Ƙasa da Cibiyar Ci Gaban Matasa ta shirya a Ɗakin Karatu na Olesegun Obasanjo dake Abekuta.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce babban abinda ya dame shi shi ne gina shugabanni da za su shugabanci nahiyar Afirka su kai ta gaci.

Ya ce Ubangiji Ya yi masa baiwa da ya raya shi tsawon shekaru bayan ya yi shugaban mulkin soja da kuma na farar hula a ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce maƙasudin Shirin Shirya Matasa na Shugaban Ƙasar shi ne a sauƙaka wa matasa su bayyana baiwarsu.

Ya lura da cewa matasa a faɗin Afirka na buƙatar su riƙa ma’amala da shugabanninsu.

Amma, ya shawarci matasan da su sadaukar da kawunansu a ɗaidaikunsu da kuma a dunƙule don ciyar da nahiyar Afirk babbar ƙasa.

Yayinda yake amsa tambayoyi daga mahalarta shirin, Mista Obasanjo ya ce: “Ba na tsoron mutuwa a shekaruna, Ubangiji Ya yi min baiwa, kuma na gode da ni’imomin da Ubangiji Ya yi min tsawon waɗannan shekaru.

“Abinda ya dame ni a tsawon shekaru shi ne gina shugabannin Afirka. Babban abinda ya dame ni shi ne gobe, kuma goben za ta fara ne daga yau.

“Duniya tana cikin rikici, na yi imanin cewa matasa na buƙatar yin ma’amala da shugabanninsu, su kuma riƙa koyo daga gare su.

“Ina son ku gane kawunanku, kuma kuma yi amfani da shaidarku wajen cimma hidima ga Ubangiji da al’umma.

“Ina son ku fito a ɗaiɗaukunku da kuma a dunƙuke wajen mayar da Najeriya da Afirka gaba ɗaya wata ƙasa babba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan