Yadda Farashin Jaki Ke Kokarin Gagarar Talaka

501

Jaki dai na daya daga cikin dabbobin dake taimakawa dan adam musamman talakawa a fannoni da dama kamar su sufuri da dako da fatauci da noma da dai sauransu, to sai dai sannu a hankali jama’a sun rage amfani da wannan dabba saboda sauyin zamani, wanda ya sanya jakunan ke dan karen tsada.

Yadda ake fitar da jakai masu tarin yawa a kowace rana daga cikin kasar nan zuwa kasar sin wato China, hakan ya sanya jakuna su ke matukar tsada a kasuwanni. Domin kuwa a shekarun baya farashin managarcin jaki ba ya wuce naira dubu talatin (₦30,000) amma yanzu lamarin ya kai babu jakin da za ka samu a kasa da wannan farashin.

Wani dillalin jaki da mu ka zanta da shi ya bayyana cewa “a shekarun baya ana samu managarcin jaki akan farashin mai rahusa da rangwame, amma shigowar yan Cana cikin harkar siyan jakuna ya yi matukar tashin farashin jakunan”

Ya kara da cewa a yanzu haka idan kana son managarcin jaki to babu shakka farashin sa na kamawa daga naira dubu 90 zuwa sama.

Sai dai wani bincike ya bayyana cewa a kasar ta China ana yin magani da fatar jakuna wanda ya ke da matukar tsada a kasar, kuma shi ne maganin da aka fi saye a shekarun baya-bayan nan.

Har ila yau naman jaki shaharrren abinci ne a kasar ta China, amma saboda karancinshi a kasar da kuma rashin yawan haihuwa akai-akai ya tilasta musu fita wasu kasashen nemo shi.

Ana amfani da dafaffiyar fatar jaki wajen hada magani Ejiao, inda suke sayer da shi kusan fam 300 duk kilo daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan