Home / Labarai / Birnin Kano Mai Abin Mamaki! Yaro Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka!

Birnin Kano Mai Abin Mamaki! Yaro Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka!

Wato akwai abubuwa a kano da suke da ɗaure kai, wasu in ka ji su, sai duk jikinka yai sanyi, wasu su yi ta baka dariya, wasu abubuwan kuma sai mutum yai ta mamaki.

Akwai wani gida ɗan nesa da gidan mu a fagge, wai shi gidan ɗumame. Shi wannan gidan ɗumamen tuwo ake siyarwa. Shi tuwon da daddare ake dafa shi, a bari ya kwana sannan a ɗumama. Ko nawa zaka bayar ba a za siyar ma da sabo ba. Sai dai ka bari in safiya tayi ka je ka siya. Kuma in har ka wuce 7:30am to zai yi matuƙar wuya ka samu.

Akwai wani gida kuma shi gidan tara. Abinci ake siyarwa, amma shi dole sai ƙarfe taran dare. Duk abun ka, ba za a siyar ma da abinci ba sai ƙarfe tara. Ko ka haƙura tara tayi, ko ka haƙura da abincin.

Akwai wani gidan kuma, shi ɗan wake ake siyarwa, in dai ka je ka ce a baka “ɗan wake” to baza a siyarma ba. Sai dai ka ce abaka “mai kodin” in ba haka sai dai ka tafi.Ka ji in da aka san darajar ɗan wake Alhaji.

Akwai wani gida ma tuwo ake siyarwa, ba za a siyarma da nama fiye da na kuɗin tuwon ba. Misali; Ba za a siyar ma da tuwon ɗari ba naman ɗari da hamsin ba.


A kullu yaumin dai kuɗin tuwo shi ne gaba da na nama. Sai dai ka siyi tuwo ɗari da hamsin naman ɗari. In ka matsa sai a ce ma nan gidan tuwo ake siyarwa ba nama ba. In za ka sai tuwo ka siya. Ka ji in da aka san darajar tuwo Malam.

Kai akwai wani mai gurasa ma da na sani in dai ka ce a baka gurasa, sam ba zai siyar ma ba, sai dai ka ce a baka “saba bread”

Kai akwai irin wannan abubuwa da yawa a Kano. Sai dai ka faɗi iya yadda ka sani kurum.

Daga Shafin Mukhtar Mudi Spikin

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *