Nasarar Ganduje: Ba Za Mu Sassauta Ba Har Sai Mun Ƙwato Haƙkinmu- PDP

517

Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano ta mayar da martani ga hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zama a Kaduna ta yi, wadda ta tabbatar da zaɓen Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano.

Labarai24 ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi watsi da ƙarar da PDP da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir-Yusuf suka shigar, inda suke ƙalubalantar hukuncin da Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Kano ta yanke, wadda ta tabbatar da nasarar Gwamna Ganduje.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 2 ga watan Oktoba ne Shugabar Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Kano, Mai Shari’a Halima Shamaki ta yi watsi da ƙarar da PDP da Mista Kabir-Yusuf suka shigar saboda rashin hujjoji.

A hukuncin nata, Mai Shari’a Shamaki ta tabbatar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta yi dai-dai da ta bayyana zaɓen 9 ga watan Maris a matsayin wanda bai kamamala ba, kuma ta yi dai-dai da ta bayyana Gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen na zagaye na biyu.

Bayan nan ne sai PDP da Mista Kabir-Yusuf suka ɗaukaka ƙara, inda suke ƙalubalantar hukuncin.

To sai dai a wani hukunci da gaba ɗaya alƙalan suka amince da shi, Mai Shari’a Tijjani Abubakar, wanda ya jagoranci gungun alƙalai biyar ya yi watsi da ƙarar ɗan takarar gwamnan na PDP gaba ɗayanta saboda rashin cancancta, ya kuma tabbatar da gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaɓen 23 ga watan Maris a jihar.

To sai dai a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Mista Kabir-Yusuf, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce jam’iyyar hamayyar ta karɓi hukuncin na Kotun Ƙoli “da matuƙar rashin jin daɗi”.

Mista Dawakin-Tofa ya ce PDP da ɗan takararta a zaɓen, Abba Kabir-Yusuf suna yin nazarin hukuncin, kuma “za su ɗauki matakin da ya dace don tabbatar da cewa sun ƙwato haƙkin da aka ƙwace”.

“Ba za mu zauna mu ƙyale ƙoƙarin da muke yi wajen samar wa mutanen da suka yii zaɓe adalci ba, mutanen da suka yi fitar ɗango suka kada ƙuri’unsu ranar Asabar 9 ga watan Maris, 2019, waɗanda aka tursasa musu, aka ba su tsoro, aka sassare su, kai har da kisa tare da hana wasu zaɓar abinda suke son zaɓa yayin zaɓen zagaye na biyu na ranar 23 ga watan Maris.

“Muna son mu yi amfani da wannan dama mu yi godiya da nuna gamsuwa ga dukkan magoya baya, waɗanda suke ta yin addu’a ba ƙaƙƙautawa a wannan gwagwarmayar shar’ia, muna ƙara tunatar da su cewa su kwantar da hankalinsu, domin ba mu da wata jiha da ta wuce Kano, zaman lafiyar Kano yana da matuƙar nuhimmanci a gare mu”, in ji shi.

Mista Dawakin-Tofa ya ƙara da cewa: “Har yanzu muna da fata a ɓangaren shari’a, duk da cewa hakan ba yana nufin ba za mu fuskanci ƙalubale a tsarin shari’ar ba, saboda haka a yanzu gwagwarmayar tana kan mataki mafi muhimmanci.

“Ba za mu kasa ko yin ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da haɓbaka abinda muka sanya a gaba, ya zama dole a kanmu mu ƙara azama har sai nasarar da muke fata ta samu. A matsayinmu na Musulmi na gari, mun sani cewa mulki na Allah ne, kuma Shi Yake bayar da shi ga wanda ya ga dama a lokacin da ya ga dama”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan