Ba Ni Da Niyyar Yin Tazarce – Shugaba Buhari

132

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen rade radin da ake cewar zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2023, inda yake cewa ba zai taba yin irin wannan kuskuren neman wa’adi na 3 ba.


Buhari ya bayyana haka ne wajen taron Majalisar zartarwar Jam’iyyar APC da ya gudana a Abuja, inda yake cewa a matsayin sa na wanda ya ranste da Al Qur’ani ba zai bari ya yi rashin hankali wajen daukar matakin karya doka ba, ganin cewa yana wa’adin sa na karshe ne.


Shugaban yace aniyar da ya sa a gaba itace yiwa talakawa aiki da kuma karfafa jam’iyyar APC, inda ya bukaci mutanen da aka zaba a matakai daban daban da su sauke nauyin dake kan su.


Buhari yace tarihi ba zai mutunta ‘yayan jam’iyyar su ba, muddin suka barta ta rushe bayan kammala wa’adin mulkin sa.


Shugaban ya kuma yaba da irin hadin kan da yake samu daga Majalisar dokoki yanzu haka, sabanin irin abinda aka gani a Majalisar da ta shude.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan