Direban Tirela Ya Kashe Ɗan KAROTA A Bakin Aiki

330

A ranar Asabar da yamma ne wani direban tirela ya take wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, inda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a Babban Gidan Mai na NNPC dake Hotoro, a cikin birnin Kano.

Majiyarmu ta ce wannan al’amari ya faru ne bayan Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, ta cafke wani direba, Alkasim Usaini, wanda shi ma ya take wani jami’in na KAROTA, Ahmad Tijjani ranar 29 ga Oktoba, yayinda yake bakin aiki.

Mai magana da yawun KAROTA, Nabulisi Kofar Na’isa ya ce jami’in, Abdurrahman Isyaku Bayero ya mutu ne bayan an kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad bayan direban tirelar ya take shi.

Mista Kofar Na’isa ya ce tuni an binne marigayi Bayero mazaunin unguwar Kwanar PRP, a Brigade, kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanada.

Ya ce tuni an kama direban tirelar aka kuma miƙa shi ga jami’an ‘yan sanda.

Ya ce Manajan Darkatan KAROTA, Baffa Babba-Danagundi, ya bayyana kaɗuwarsa yayinda yake yi wa iyalan marigayin ta’aziyya.

Mista Babba-Danagundi ya gargaɗi mutane da su guji kai wa jami’an KAROTA hari.

Ya ce za a hukunta dukkan masu laifin kamar yadda doka ta tanada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan