Kano Pillars na Cikin Tsaka Mai Wuya Bayan 0 – 0 da Wikki

269

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na cikin tsaka mai wuya bayan sun buga kunnen doki da Wikki Tourist na garin Bauchi.

Wasan dai antashi kunnen doki wato babu ci tsakaninsu.

Tun a makon daya gabata mahukuntan kungiyar ta Kano Pillars suka baiwa masu horas da kungiyar adadin wasanni guda 3.

Yanzu dai Pillars sun buga wasanni biyu daga cikin ukun inda Jigawa ta casa Pillars din atsakiyar makonnan sai kuma yau suka buga kunnen doki da Wikki Tourist.

Yanzu dai an buga wasannin mako na 5 amma Pillars bata lashe ko wasa daya ba inda kusan hakan bai taba faruwa ba akan kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars.

Awasan mako na 6 dai Pillars zata kaiwa Plateau United ziyara a garin Jos inda ayau dinma Plateau United din ta lallasa Delta Force har gida daci 3 da 1 kuma sune suke jan ragamar teburin da maki 13.

Shin ko menene makomar masu horas da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars matukar suka kammala wasanninsu guda uku batare da nasara ba?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan