Yaudara Tushen Matsalar Rayuwa – Jiddah Gaya

638

Yaudara wata dabi’a ce da za’a iya cewa ta zama ruwan dare a tsakanin matasa samari da yanmata a harkar soyayya. Yaudara na tafiya kafada da kafada da karya, domin shi mayaudari ko mayaudariya ba ka rabasu da karya kullum cikinta su ke.

Hadisi ya tabbata cewa; abubuwa guda uku idan mutum ya kasance yana aikata su to shi din munafiki ne: Idan yayi alkawari ya saba, Idan yayi zance yayi karya, Idan an amince masa yayi ha’inci. Wadannan suffofi duk ana samun su a wajen mayaudari, to kaga baya ga shifata karya a iya karawa da sifar munafirci. Abin takaici a kullum sabbin hanyoyi da dabaru matasa ke fito dasu na yaudara.

Haka kuma, a ko da yaushe bangare daya na daura wa daya bangaren laifi, ma’ana samari na kallon laifin akan yanmata suma yanmatan na yi musu kllon laifin akan samarin ya ke.

Ita wannan dabi’a ta yaudara, ta kasu kashi-kashi. Ko wani bangare da salon yadda suke yin tasu yaudarar, amma mafi girman yaudara itace mutum ya aminta da kai dari bisa dari daga karshe sakamakon yaudara ya biyo baya.

Salo ko nau’in yaudarar da Samari ke yi sun hada da: zuwar wa mace da nufin aurenta zakayi tare da nuna mata soyyaya irin wacce zaiyi wuya wani bama ita ba ya gane cewa yaudara ce ta kawo ka, saboda kazo da fari cikin sigar da zaiyi wuya a gano manufarka. Sai tafiya tayi tafiya in ka fara baiyana hakikanin manufarka sai ta fara kokonton soyayyar taka a gareta. Akan yi rashin sa’a maza masu irin wannan sigar yaudarar su cimma manufarsu akan yarinya sakamakon gadar zaren da suka kulla mata tun a fari, daga karshe yayi watsi da ita. Wannan itace mafi muni yaudarar da maza ke yiwa mata.

Salo na biyu shi ne, saurayi yazo da karyar shi wani ne, walau shi mai kudi ne ko iyayensa wasu ne ko kuma yana wani aiki mai kyau, masu irin wannan salon na samun nasara ne har a amince musu idan yarinyar makwadaiciya ce kuma ya hadu da Iyayen da basa zurfafa bincike.

Salon yaudara ta uku wadda kusan da wuya a samu saurayin da baya ko kuma bai taba irin wannan ba: hada yanmata masu yawa a lokaci guda kuma ka nuna wa kowacce aurenta kake son yi wanda daga karshe ba lallai ya aure ko da guda daga cikinsu ba.

To, a bangaren mata ma ana samun masu wanna dabi’a, amma ita mafi munin yaudarar da mace zata yiwa saurayi itace; nuna masa cewa dari bisa dari ta amince da soyayyar sa kuma zata aure shi, daga bisa ni kuma sai ta gujeshi.

Salon yaudara ta biyu Kwatankwacin irin yaudarar da maza keyi ce na tara yanmata. Suma matan akwai masu irin wannan dabi’a su tara samari a lokaci guda kuma kowanne a nuna masa ana kaunarsa kuma za’a aure shi.

To, yaudara dai ba abace mai kyau ba, kuma mafi yawa mayaudari ko mayaudariya na fadawa yanayi maras dadi koda ya cimma abinda yake so.

Har kullum dai ana so duk abinda mutum zaiyi to yayi shi bisa kyakkyawar niyya da kuma sa tsoron Allah a ciki. Shi makasudin wannan alaka ta samari da yanmata domin a kulla aure ne. Aure ibada ne ba wai jin dadi ba, duk da cewa akwai jin dadin amma in aka kyautata shi.

Ya kamata matasa musan shi dai auren nan ibada ce kamar sauran ibadu, yana da kyau kamar yadda kake kyautata sauran idadu aure shima ya samu wannan kyautatawar.

Jiddah Gaya, Yar Jarida Ce Mai Yin Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Ta Rubuto Daga Birnin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan