Ahmad Tijjani Musa: Shugaban Karamar Hukuma Mafi Kwazo A Jihar Kano

291

Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada, da ke Jihar Kano Alhaji Ahmad Tijjani Musa da lambar yabo na wanda ya fi dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Kano a fannin raya tattalin arzikin al’ummarsa tare da samar musu da sana’o’in dogaro da kai.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, yan siyasa da kuma masu rike da sarautun gargajiya.

Idan za’a iya tunawa ko a cikin watan Oktoba sai da kungiyar Grassroots Sports Federation da ke Kaduna ta karrama shi a matsayin shugaban karamar hukuma mai kwazo

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan