An Gudanar Da Gangamin Ranar Yaki Da Cin Zarafin Mata Ta Duniya A Kano

560

Wata kungiya mai taken North normal ta gudanar da wata zanga-zangar lumana farfajiyar zauren majalisar dokokin jihar Kano.

Tun da farko kungiyar ta gudanar da wannan zanga-zangar ne a matsayin gangamin bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.

Da ta ke jawabin dalilin gudanar da wannan zanga-zangar, Zainab Naseer Ahmed ta bayyana cewa sun yi amfani da wannan rana ne domin tunawa majalisar dokokin jihar Kano akan ta sanya hannu akan dokar cin zarafin mata.

A nasa bangaren Akawun majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Alfa Hausawa, ya bayyana goyon bayan majalisar akan wannan gangami tare da yin alkawarin gabatar da bukatarsu a gaban kakakin majalisar dokokin jihar Kano.

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 25 ga watan Nuwamban kowace shekara domin tunawa da matsalar cin zarafin mata a kasashen duniya.

A cewar Majalisar matsalar babban ce a tsakanin al’umomi daban-daban na duniya, da ke tauye ‘yancin mata ta fuskar ilimi da kiwon lafiya da tattalin arziki da kuma zamantakewa.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa mace daya cikin mata uku ta taba fuskantar wani nau’i na cin zarafi walau fyade ko duka ko musgunawa ko auren wuri ko kuma kaciya.


An fitar da wadannan alkaluman ne, don bankado dukkan nau’ukan cin zarafi da duniya ba ta farga da su ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan