Home / Labarai / Jirgin Ruwa Dauke Da Raguna 14,000 Ya Kife A Gabar Tekun Romania

Jirgin Ruwa Dauke Da Raguna 14,000 Ya Kife A Gabar Tekun Romania

Wani katafara jirgin ruwa mai dakon kaya da ya ke dauke da raguna da tumaki 14,000 ya jirkice a kusa da gabar tekun kasar Romania.
Masu ceto na can ana kokarin ceto dabbobin daga mawuyacin halin da suka sami kansu.


Jirgin Queen Hind ya kwanta gefe guda ne a cikin teku da safiyar Lahadi bayan ya bar tashar jirgin ruwa ta Midia a kusa da birnin Constanta da ke kudu maso gabashin kasar Romania.


Tuni aka ceto matukan jirgin da ma’aikata 22 wadanda daukacinsu ‘yan asalin kasar Syria ne.


A halin da ake ciki, akwai wata tawaga ta jjami’ai masu cetto da ta hada da ‘yan sanda da ‘yan kwana-kwana da dakaru masu tsaron gabar tekun Romania da suke ayyukan ceto dabbobin.


Amma duk da wannan kokarin, wasu dabbobin sun mutu a cikin ruwan tekun bayan sun fada ciki, amma an ceto 32 cikinsu.


Stoica Anamaria ce kakakin dakarun tsaron gabar tekun Romaia, kuma ta fada wa BBC cewa: “Tuni muka ceto wasu dabbobi kalilan daga teku.”


Za a ci gaba da ayyukan ceto raguna da tumakin da safiyar Litinin.


Daya daga ciin matuka jirgin na asibiti saboda sanyi bayan ya fada cikin ruwan teku.


Ba dai san dalilan da suka janyo wannan hadarin ba, amma za a gudanar cikakken bincike bayan an kammala ceto dabbobin kuma an tsamo jirgin daga teku.

Rahoton BBC Hausa

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *