Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Saminu Turaki Ya Kara Aure

472

Wasu hotunan tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, tare da Amaryarsa da su ke ta zagaya kafafen sada zumunta sun ja hankalin al’umma musamman masu amfani da shafin sada zumunta na fasebuk.

Tun da farko wani makusancin gwamnan ne mai suna MD Usman Abdullahi Babura ya wallafa hotunan tsohon gwamnan tare da wata mata, wacce alamu su ke nuni da ita ce amaryar, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, a shafinsa na fasebuk.

An dade dai ba’a ji duriyar tsohon gwamnan a harkar siyasar kasar nan, tun bayan da wata kotu ta bayar da belinsa a cikin shekarar 2017 bayan hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin wawure naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulkin jihar Jigawa.
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan