Ganduje Ya Rushe Kangon Sarki Sanusi Na Miliyan 250

1172

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙwace tare da rushe wani fili da kuɗinsa ya kai miliyan M250 mallakin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, sannan ta bada izinin a ba shi miliyan 4.5 a matsayin diyya.

Wani binciken haɗin gwiwa da jaridun DAILY NIGERIAN da KANO FOCUS suka gudanar ya nuna cewa filin, wanda yake a kan Titin Ibrahim Dabo, an rushe shi ne don a samar da hanya a aikin ginin gadar sama da ta ƙasa da ake yi a Shatale-Talen Dangi.

Akwai rashin jituwa tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin, abinda ya haifar da rage tasirin Sarki Sanusi ta hanyar ƙirƙirar sabbin masarautu huɗu da kuma sarakuna masu daraja ta ɗaya a Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya.

A makon da ya gabata, Babbar Kotun Kano ta soke dokar da ta ƙirƙiri sabbin masarautun, abinda ya jawo aka fara tsoran cewa hukuncin zai iya zafafa rikicin.

Wakilan DAILY NIGERIAN da KANO FOCUS sun ruwaito cewa Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’az Majaji da kansa ya duba ƙwace filin da rushe gine-ginen da suke cikin filin da katangar da ta zagaye filin a ranar Juma’a, 15 ga Nuwamba, 2019.

Jami’an Ma’aikatar Ƙasa ta Jihar Kano waɗanda suka tattauna da wakilan waɗannan jaridu biyu bisa sharaɗin za a sakaye sunayensu sun ce Sarki Sanusi ya sayi filin mai tsawon hekta 1.2 a shekarar 2010 a kan kuɗi naira miliyan N200.

A ta bakinsu, kwanan nan aka yi wa filin kima a kan miliyan N250 a wajen ‘yan kasuwa, amma gwamnatin jihar ta dage kan cewa za a biya diyyar ne kamar yadda dokar filaye ta tanada.

An gano cewa Mista Magaji, bisa rakiyar wata babbar tawagar matasa ‘yan daba ɗauke da makamai, shi ya jagoranci jami’an ma’aikatarsa zuwa filin na Sarki Sanusi, inda da kansa ya hau motar rushe gini, Grade D9, ya rushe wani sashi na katangar da ta zagaye filin.

Wakilan jaridun sun gano cewa kafin Mista Magaji ya rushe katangar, ya buƙaci Sarkin da ya aiko da wakilai da za su duba aikin rushe filin- buƙatar da Sarki Sanusi ya yi biyayya ta hanyar aika Hakimin Garko wanda ya wakilce shi.

A cewar shaidun gani da ido, bayan kwamishinan ya rushe wani sashi na katangar filin basaraken a gaban wakilinsa, sai ya umarci gungun ‘yan daban dake jira da su kwashi ganima a filin.

Shaidun suka ƙara da cewa Mista Magaji ya kuma juyo, sannan ya saita motar rushe ginin zuwa jerin wasu shaguna dake kusa da gadar da ba a kammala gininta ba, ya rushe wani ɓangare na shagunan, kafin daga bisani ya umarci ‘yan daban da su kwashi “ganinmarsu”, yana mai cewa an biya masu shagunan cikakkiyar diyya.

Lokacin da aka tuntuɓe shi, Shugaban Ma’aikatan Sarkin, Munir Sanusi, ya ƙi cewa uffan game da maganar, yana mai cewa Sarkin bai ba shi izinin ya yi magana ba.

Amma, majiyoyin fada sun ce har yanzu Sarkin bai karɓi ko ficika ba daga gwamnatin a matsayin diyyar filin, wanda hanya za ta bi ta cikinsa.

Amma, a waya tattaunawa ta waya da ɗaya daga cikin wakilan jaridun, kwamishinan ya yi ikirarin cewa gwamnati ta biya Sarkin diyya.

“Ina mai tabbatar maka ya samu saƙon shigar kuɗi. Tsawon wata takwas, wannan batu ya tsayar da aikin, kuma wannan aiki ne na al’umma.

“Mun yi ta fatan ma ko Sarkin zai bayar da filin kyauta don a ci gaba da aikin. Amma tunda bai ba mu ba, sai muka yanke shawarar tuntuɓar masana darajar ƙasa, waɗanda suka yi masa kima dai-dai da dokar filaye saboda gwamnati ba kasuwanci take yi ba”, a kalaman kwamishinan.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa shi da kansa ya hau Grade D9 Bulldozer don rushe gine-ginen da ake magana a kai.

Ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta kammala biyan diyya ga dukkan masu filaye waɗanda aikin gadar saman ya shafi gine-ginesu.

Hukumomin Masallacin Umar bin Khattab Su Ma Sun Koka

Haka kuma, Malam Mu’azu Shu’aibu, Sakatare Janar na Gidauniyar Musulunci- wata ƙungiya da ba ta gwamnati ba wadda ke mallakar filayen da shagunan da aikin gadar ya shafa ke ciki, shi ma ya zargi gwamnatin jihar da ƙwace musu filaye ba tare da biyan diyya ba.

Mista Shuaibu ya bayyana cewa an ba masu hada-hadar hayar filayen ne bisa tsarin Gina, Bada Haya da Dawo Da Shi, BOT, na tsawon shekaru 20, da nufin samun kuɗin da za a tafiyar da Masallacin Umar bin Khattab.

Ya ce jami’an gwamnatin jihar sun same su lokacin da aka fara aikin ginin, kuma suka faɗa musu cewa awo ya nuna cewa aikin zai shafi filayensu.

“Sun turo masana darajar ƙasa don su auna suga nawa ya kamata a ba duk mai fili. Amma muka faɗa musu cewa ba za su ci gaba da rushe gine-ginen ba har sai an biya masu shagunan diyya.

“To, sai suka buƙace mu da mu tura musu lambobin asusun ajuyarmu na banki, amma muka ce a’a, ba za mu iya tura lambobin asusun ajiyarmu na banki ba har sun faɗi alƙaluman da kowane mai shago zai samu.

“Bayan an ɗauki lokaci, sai jami’an gwamnatin suka aiko da alƙaluman, mu kuma muka nuna wa dillalanmu kafin daga ƙarshe mu tura lambobin asusunmu, daga nan jami’an gwamnatin suka ce mu jira za a biya”, in ji shi.

Mista Shuaibu ya ce a yayinda Gidauniyar Musuluncin da dillalan filayen ke jiran diyyar, sai ya samu wata wasiƙa da Dahiru Ada’u, Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ya sanya wa hannu, inda yake neman haɗin kai don ya kaɓi filin.

“Duba da buƙatar kammala wannan muhimmin aiki a kan lokaci don amfanin ɗimbin al’ummar jihar, na rubuto wannan wasiƙa don sanar da kai cewa wannan ma’aikata ta shirya karɓar sashin da aka tsara don ci gaba da aiwatar da aikin.

“Bisa wannan, za a fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba ranar Juma’a, 15 ga Nuwamba, 2019. Saboda wannan abu da aka ambata ne nake neman haɗin kan da ka saba bayarwa don kammala aikin cikin nasara kuma a kan lokaci, wanda zai kawo ƙarshen matsalolin cunkoson ababen hawa a babban birninmu”, wani ɓangare na wasiƙar ya bayyana haka.

Ya ƙara bayyana cewa jim kaɗan da karɓar wasiƙar da ya yi, sai ya ji sanarwa cewa an biya diyya, kuma an ba masu shaguna sa’o’i 24 su tashi su bar shagunan.

“Sai na tubtuɓi dillalan don jin ko wani daga cikinsu ya samu saƙon shigar kuɗi, amma gaba ɗaya suka ce ba su karɓi saƙonnin shigar kuɗi ba. A ƙasa da sa’o’i 24, kwamishinan ya zo da kansa ya fara rushe ɓangaren shagunan, daga nan kuma ya umarci ‘yan daba da su kwashe komai a matsayin ganima, yana mai iƙirarin cewa sun biya diyya”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan