Home / Labarai / Ina Son Na Zama ‘Yar Kasuwa Tamkar Aliko Dangote –Sadiya Kabala

Ina Son Na Zama ‘Yar Kasuwa Tamkar Aliko Dangote –Sadiya Kabala

Jarumar fina-finan Hausa Sadiya Kabala ta bayyana cewa burinta shi ne ta zama ‘yar kasuwa mai kudi kamar Alhaji Aliko Dangote.

Sadiya Kabala ta wallafa a shafinta na Instagram cewa ”Mafarki na shi ne in zama ‘yar kasuwa kamar Dangote nima wata kila a kirani ‘Yargote”

Wannan batu na jurumar dai ya sanya cecekuce tsakanin mabiyanta, wadanda suka rika bayyana mabam-bamtan ra’ayoyi akai, yayin da wasu ke mata fatan alkhairi, wasu kuwa tuni ma suka fara kiranta da ‘Yargote.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jaruman masana’antar Kannywood ke fatan zamowa ‘yan kasuwa ba, domin kuwa ko a baya-bayan nan matashiyar jaruma Maryam Yahya ta bude shagon kasuwanci a Kano.

Haka kuma ko a makon da ya gabata a wata tattaunawa da jarumi Ali Nuhu yayi da sashen hausa na BBC ya bayyana cewar shi ma yana hadawa da wasu sana’o’in baya ga harkar sa ta wasan kwaikwayo.


Rahotoan Freedom Radio Kano,

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *