Kaf Kabilun Najeriya Babu Mai Wulakantar Da Mata Kamar Bahaushe – Rabi Salisu Ibrahim

3208

An bayyana Malam Bahaushe a matsayin wani mutum wanda yake tozartawa gami da cin zarafin mata da sunan aure, a tsakanin sauran jinsinan jama’ar kasar nan gaba daya.

Shugabar cibiyar ARRIDAH Foundation dake Kaduna Hajiya Rabi Salisu Ibrahim ce ta bayyana hakan, lokacin wata tattaunawa da manema dangane da batun dokar haramta karin aure da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, ya gabatar a birnin Kano.

Hajiya Rabi Ibrahim ta cigaba da cewar, babban abin mamaki ya kare akan Malam Bahaushe, wanda shi a rayuwarshi babu abinda ya tsare illa batun aure-aure, ya tara Mata hudu a gidan haya cikin talauci, yayin da iyali sukayi yawa a fara ina za’a sa ka dasu, karshen lamari a tattarasu a mikawa wani Malamin allo da sunan almajiranci, batun tarbiyarsu kuwa ko oho.

Shugabar cibiyar ta Arridah tace lallai ne ya zama wajibi ga dukkanin wani mai hankali daya goyi da bayan wannan kuduri da mai martaba sarkin kano ya bijiro dashi na haramta karin aure akan Hausawa matalauta, domin shine zai kara tabbatar da daraja da kare kimar mata a kasar hausa, wadanda aka daukesu tamkar wasu kayan sawa, kasa lokacin da kake bukata, ka ciresu kuma lokacin da kake bukata.

Hajiya Rabi ta kuma soki lamirin wani hadisi na hausawa dake cewar wai bakin da Allah ya tsaga baya hana mishi abinci, inda tace wannan kalami na hausawa ya ci karo da tsari na rayuwa, domin babu inda Allah yace kaje ka dauko nauyin da baza ka iya saukewa ba, inda ta kara shawartar al’ummar hausawa dasu guji kawo tarnaki da cikas a duk lokacin da aka bijiro da wani batu na cigaba, musanman akan abinda ya shafi cigaban mata.

Hajiya Rabi ta kuma soki lamirin rubuce-rubucen da wasu hausawa masu adawa da batun Sarkin Kano sukeyi a kafafen sadarwa na zamani, inda suke fadin cewar wai da zina cikin wadata gwamma aure cikin talauci, inda ta bayyana cewar wannan magana ba gaskiya bane, domin mata da dama kamar zawarawa dama wasu ‘yan matan talauci na jefasu cikin wani hali na kauce hanya na zinar talauci, ashe ya dace mu fahimci hikima ta mai martaba sarki akan wannan batu daya kawo, kasancewarshi mai digirin digirgir a fannin shari’ar musulunci.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Bata san kabilun najeriyabane sannan may be tana fadin halin gidansu ne ko gidan mijinta, amma data san kabilun najeriya da bata fadi haka ba koda dai son zuciya da neman suna yakan isa sawa a fadi komai, yar uwa bahaushene ya dauki ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da bada wurin zama a matsayin wajibi a aure kuma yake kokarin hakan sannan matar bata ganin kokarinsa amma bai fasa ba don yasan hakan addinine kuma nasan ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba rashin sanin darajar miji wannan nema yasa kike fadi haka don da kin san darajar miji da gode masa wlh bazaki fadi haka ba, Allah shiryar dake yasa ki zamo mai godiya wa Allah da kin huta kuma kin samo rabon lahira,Allah shiryar damu mu gane daidai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan