Mafiya Yawan ‘Yan Siyasar Najeriya Ba Su Yi Imani Da Allah Ba- Tsav

257

Tsohon Kwamishina ‘Yan Sanda na Jihar Legas, Abubakar Tsav, ya ce mafiya yawan ‘yan siyasar Najeriya ba su yi imani da Allah ba.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa aka kuma ba Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Makurɗi ranar Talata.

“‘Yan siyasarmu ba su yi imani da Allah ba da kuma yadda wannan duniya take ba a bakin komai ba. Ba sa ma tunanin mutuwa.

“Dimokuraɗiyyarmu ta zama wani abu daban. Kamar ba mu san abinda dimokuraɗiyya take nufi ba.

“Da yawa suna kallonta a matsayin wata hanya ta tara dukiya ta hayar damfara da rashin gaskiya”, in ji Mista Tsav.

Ya ce indai kotuna ba su tashi tsaye wajen gaggauta hukunci ga mutanen da ake zargi da cin hanci ba don hakan ya zama darasi ga saura, da yawa za su ci gaba da zama dumu-dumu a cikin cin hanci.

Mista Tsav ya ce yin Allah-wadai kawai ba tare da hukuncin da doka ta tanada ba ba zai hana cin hanci ba a ƙasar nan.

“Yaƙin da ake yi da cin hanci ba shi da tasiri a kan al’ummarmu, shi yasa har yanzu ‘yan siyasa ke yaƙa tare da kashe juna don samun muƙaman siyasa.

“Idan kotuna suka gaggauta yanke hukunci ga mutanen da ake zargi da cin hanci a kotuna daban-daban, wata ƙila halin da za su shiga zai zama darasi ga wasu.

“Wannan zai taƙaita buƙata da haukan cin hanci”, in ji shi.

Mista Tsav ya ƙara da cewa abubuwan da suka faru a zaɓen gwamnan Kogi da aka yi kwanan nan sun nuna cewa lokaci ya yi da za a yi wa dokokin zaɓe kwaskwarima don samar da hukunci mai tsauri ga masu aikata laifukan zaɓe.

Ya kuma yi Allah-wadai da kashe Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP a jihar Kogi bayan kammala zaɓen, yana mai bayyana hakan a matsayin wani abu mafi tayar da hankali da ya ji kwanan nan.

“Na yi farin ciki da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan wannan mummunan aiki don a gano duk waɗanda ke da hannu, a gurfanar da su a gaban shar’ia, duk matsayinsu.

“Ya kamata Buhari ya yi fiye da haka. Ya kamata a gyara dokokin zaɓe don dimokuraɗiyya ta gaskiya ta samu gindin zama.

“Abinda ya fi sa ni baƙin ciki a lokacin da nake aiki da Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, shi ne inda gwamnati take da sha’awa a wani abu, irin waɗannan abubuwa ba sa kammaluwa, kada a bar wannan ya faru a nan fa”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan