Marasa Kishin Ƙasa Na Yi Min Zagon Ƙasa- Pantami

271

Dakta Isa Pantami, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, ya yi gargaɗi bisa zagon ƙasa da wasu da ya kira “marasa kishin ƙasa”ke yi a asirce don hana Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Mista Pantami ya yi wannan gargaɗi ne a cikin wata sanarwa da Uwa Suleiman, mai magana da yawunsa ta fitar ranar Litinin a Abuja.

A cewar sanarwar, binciken da ake yi wa masu masu tabon cin hanci ya bayyana irin mugun tanadin da suke yi wa ma’aikatar.

Ministan ya ce mutanen da abin ya shafa sun fara wannan kamfe ne saboda ba sa jin daɗin manufofinsa na hidimta wa al’umma, kuma da yadda aka hana su su ci gaba da cin karensu ba babbaka.

“Dabarar da waɗannan ɗaiɗaikun mutane suke yi shi ne su haɗa kai da kafafen yaɗa labarai, ta hanyar amfani da ‘yan kuɗaɗe, kuma sun tara kuɗaɗe masu yawa don gudanar da wannan kamfe.

“Manufar wannan munafunci shi ne a tsorata mu mu ƙyale kamfanonin sadarwa su ci gaba da zaluntar ‘yan Najeriya”, in ji shi.

A ta bakin ministan, ma’aikatar na ci gaba da fito da manufofi don kare abokan huɗɗar kamfanonin sadarwa ta kuma kawo ɗa’a da ƙwarewa a ɓangaren sadarwa.

“Wannan mataki ya ɓata wa wasu mutane rai, waɗanda burinsu shi ne su lalata manufofin kyatata wa al’umma”, a kalamansa.

Ya yi kira ga ‘yan jarida da su yi watsi da ake yi don ɓata musu aikinsu, su kuma yi ƙoƙarin kiyaye mutuncin aikinsu.

Mista Pantami ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da ruƙo da shirinta dai-dai da manufofi uku na gwamnati mai ci, yana mai ƙarawa da cewa “ba za a ƙyale cin hanci ko rashin adalci ba”.

“Munafukai ko wakilai masu muguwar manufa ba za su tsorata mu ba, ko kuma su razana mu mu miƙa wuya.

“Nauyi ya rataya a wuyana wajen fito da manufofi da ba za su nuna bambanci ba don amfanin dukkan kowane ɗan Najeriya, mu tabbatar da cewa an kare abokan cinikin kamfanoni daga zalunci, a kuma samar da kyakkyawan muhalli ga masu zuba jari da masu kamfanonin.

Ya yi alƙawarin warware matsalar dogara da masu lura da kamfanonin sadarwa suka yi da masu kamfanonin don masu kula da kamfanonin su yi aikinsu “ba tare da son zuciya ba”.

Ministan ya yi kira ga al’umma da su zama cikin shiri bisa aikace-aikacen rashin gaskiya na waɗannan mutane ma’abota cin hanci, su kuma yi watsi da duk wata sanarwa da ta ci karo da manufofin ma’aikatar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan