Wayewar Kai Irin Ta Turawa Na Lalata Al’adun Afirka Na Girmama Manya – Buhari

255

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce abin takaici ne yadda wayewar kai irin ta Turawa ke lalata al’adun Afirka na girmama manya, da kuma yadda abin ke kara ta’azzara.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron kungiyar Kasashen Afirka Ta yamma ECOWAS, a ranar Litinin.

Ana taro ne don yin muhawarar kan batun inganta rayuwar tsofaffi a kasashen Afirka.

Ministan Ayyuka na Musamman George Akume ne ya wakilci Shugaba Buhari a wajen taron, wanda ake yi na yini biyu a Abuja, babban birnin tarayyya.

”Saboda ci gaba da wayewa irin ta Turawa, al’adunmu da suke koya mana girmama manyanmu a yanzu suna gurbacewa.

”Hakki ne a kanmu mu dawo da martabar manyanmu don ba zai yiwu mu zauna muna kallon wasu suna yin abin da mu ya kamata a ce mun yi ba,” ” a cewarsa.

Mahalarta taron dai sun fito ne daga kungiyoyi daban-daban masu ruwa da tsaki ta bangaren kare hakkin dan’adam ta fuskar inganta rayuwar tsoffi a nahiyar Afirka.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan