EFCC Ta Yi Awon Gaba Da Shugaban Gidan Yarin Kirikiri

245


An cafke shugaban ɗaya daga cikin gidajen yarin Najeriya mafi girma, wato Kirikiri, da kuma Shugaban Asibitin Gidan Yarin.

Hukumar EFCC ta cafke Emmanuel Oluwaniyi da Hemeson Edwin bisa zargin su da sakin Hope Aroke, wani ɗan damfara a Intanet wanda ke zaman cin sarƙa na tsawon shekaru 24 don a duba lafiyarsa a waje bayan kuma lafiyarsa ƙalau.

Dukkan mutanen biyu Mataimaka Kwnaturola ne a Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa, NCS.

Mista Oluwaniyi shi ne Kwanturola na Gidan Yarin Kirikiri, yayinda Mista Edwin yake a matsayin Shugaban Asibitin Gidan Yarin.

A makon da ya gabata, majiyarmu ta bada rahoton yadda EFCC ta ce duk da cewa Mista Aroke yana ɗaure a halin yanzu, amma yakan halarci bukukuwa da kuma karɓar baƙi a wani otel. An kuma same shi yana amfani asusun bankuna a cikin gidan yarin, inda har ya iya yin wata damfarar ta dalar Amurka miliyan $1.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan