Fiye Da Yara Miliyan Biyu Ba Sa Zuwa Makaranta A Katsina Da Kano- UNICEF

221

Asusun Tallafa wa Ilimin Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce a ƙalla yara 946,000 ne ba sa zuwa makarantun Boko a jihar Katsina.

Babban Jami’in UNICEF na Kano, Maulid Warfa ya bayyana haka ranar Laraba a Katsina a yayin taron bita na ƙarshen shekarar 2019.

Ya ce a jihar Kano yara miliyan 1.49 ne ba sa zuwa makarantar Boko, adadi mafi yawa a faɗin Najeriya.

A ta bakinsa, malami 1 a Kano yana lura da yara 103, a Katsina kuma, malami 1 yana lura da yara 92.

Ta ɓangaren abinci mai gina jiki, Mista Warfa ya ce kaso 60 cikin ɗari na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar na fama da rashin girma, yayinda kaso 1.7 cikin ɗari, adadin da yake wakiltar yara 423,934 na fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a jihar Kano.

Ya ce a Katsina kuma, kaso 62 cikin ɗari na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar na fama da rashin girma, yayinda kaso 2.1 cikin ɗari, adadin dake wakiltar yara 312,182 na fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

Game da Ruwa, Tsaftar Muhalli da Kiwon Lafiya, WASH, ya ce ce kaso 57.9 cikin ɗari na al’umma a jihar Kano nada damar samun kyakkyawan ruwan sha a wannan shekara.

Mista Warfa ya ƙara da cewa kaso uku cikin ɗari na al’ummar jihar Kano na yin bahaya a fili, wanda ya ce ya yi ƙasa da matakin ƙasa.

Ya yi bayanin cewa a jihar Katsina, kaso 59.3 cikin ɗari na al’umma suna da damar samun kyakkyawan ruwan sha.

Jami’in ya ci gaba da cewa kaso 53.1 na gidajen jihar Katsina suna da kayayyakin tsaftace muhalli

A kan lafiya, Mista Warfa ya ce jihar Kano ta samu adadin mata dake mutuwa a lokacin haihuwa mafi yawa, yayinda jihar Katsina kuma ta ɗan samu ci gaba a ɓangaren a wannan shekara.

Ya ce maƙasudin taron tattaunawar shi ne a yi bitar alamomin ci gaba na 2019 a jihohin biyu, don a ƙara ƙoƙari a wuraren da ya zama wajibi.

Jami’in na UNICEF ya ce mahalarta taron za su fito da matsalolin da a ka samu a 2019, a kuma shirya dabarar yadda za a yi nasara a 2020.

A jawabinsa tunda farko, Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsara Tattalin Arziƙi na Jihar Katsina, Isyaku Ahmed, ya ce gwamnatin jihar ta ware biliyan N1 a matsayin kuɗin tallafi ga aikace-aikacen UNICEF a 2020.

Ya ce kasafin kuɗin yana zauren Majalisar Dokokin Jihar don tattaunawa da sahalewa.

Mista Ahmed ya ce wuraren da kasafin kuɗin zai taɓo sun haɗa da ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki da ruwa da tsaftar muhalli.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware miliyan N123.7 ga ɓangaren lafiya, yayinda aka ware wa abinci mai gina jiki, ilimi, ruwa da tsaftar muhalli miliyan N432, miliyan N86 da miliyan N400 kowannesu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan