Gwamnonin APC 3 Da Za Su Iya Gadar Shugaba Buhari A Zaben 2023

414

A daidai lokacin da har yanzu ba a cika shekara da fara zango na biyu na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, tuni an fara mayar da hankali a kan waye zai maye gurbin Buhari a zaben shekarar 2023.


Masu nazarin siyasar kasar nan sun yi tsokaci tare da yin hasashen cewa wasu gwamnoni kan iya samun nasarar maye gurbin shugaba Buhari a zabe na gaba.


Gwamnonin uku da aka bayyana cewa za su iya gadon kujerar mulkin kasar nan daga hannun shugaba Buhari sun hada:

 1. Malam Nasir El-Rufa’i (Gwamnan jihar Kaduna): Tuni wasu kungiyoyin matasa sun fara bude ofisoshin yakin neman gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
  Ana zargin cewa El-Rufa’i yana son arewa ta kara yin takarar shugaban kasa a 2023 saboda yana son samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
 2. Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Gwamnan jihar Kano): Duk da ba kasafai ake saka shi a cikin ‘yan siyasar arewa maso son kujerar shugaban kasa ba, akwai masu ra’ayin cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kan iya samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a shekarar 2023.
  Masu wannan ra’ayi sun bayyana cewa, siyasar kasar nan na da sarkakiya. Sun fadi hakan ne saboda sanin cewa akwai wasu faya-fayan bidiyo da aka wallafa a wata jarida, in da a cikinsu ake zargin gwamna Ganduje ne ke karbar cin hanci.
  Amma duk da hakan, masu ra’ayin Ganduje zai iya samun takara, suna kafa hujja ne da biyayya da kaunar da Ganduje ke yi wa Buhari. A ganinsu, Buhari zai so ya mika takara ga wanda zai kasance mai biyayya gare shi kuma dattijo.

Sannan suna kara kafa hujja da cewa Ganduje ya bawa Buhari da APC babbar gudunmawa a nasarar da suka samu a zaben 2019, a saboda haka za a iya bashi tikitin takara domin a yi masa sakayya.

 1. Kayeode Fayemi (Gwamnan jihar Ekiti): Shi, ne shugaban zauren gwamnonin kasar nan, Kayode Fayemi na jihar Ekiti. Tsohon ministan an zabe shi ne a matsayin shugaban gwamnonin kasar nan karkashin kakkarfan mulkin shugaba Buhari, in da ya gaji Gwamna Abdulaziz yari na jihar Zamfara .
  Wasu masu kiyasi a fannin siyasar sun yadda cewa, za ta iya yuwuwa Fayemi ne mutumin da arewa zata ba goyon baya domin maye gurbin burin da Asiwaju Bola Tinubu. Arewa na ganin cewa, tsohon gwamnan jihar Legas din zai iya zama barazana a garesu wajen kwace ikon kasar nan. A don haka ne zasu iya amincewa da wanda bai kai shi buri ba kamar Fayemi a maimakon Jagaban jam’iyyar APC.
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan