Malaman Kano Poly Za Su Tsunduma Yajin Aiki

274

Malaman Makarantar Nazarin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano za su fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako ɗaya bisa matsalolin ciyar da su gaba.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Shugaban Ƙungiyar Malaman Makarantun Nazarin Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa, ASUP, Reshen Jihar Kano, Ahmad Zubairu-Chedi, ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Kano.

Mista Zubairu-Chedi ya ce ASUP za ta fasa tafiya yajin aikin idan ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano ya amince da Tsarin Aiki na 2013 da Hukumar Kula da Makarantun Nazarin Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa, NBTE, ta amince da shi.

“Shugaban Ma’aikata ya aiko da wasiƙar bayani zuwa ga NBTE ranar 14 ga watan Agusta game da aiwatar da Tsarin Aiki na 2013, wanda Babban Sakataren Hukumar ya bada amsa.

“Har kawo yanzu ba mu karɓi kwafin wasiƙar ba game da bayanin duk da mun cimma matsaya cewa duk abinda ya zo daga NBTE zai yi aiki a kan ƙungiyar da kuma gwamnati”, in ji shi.

ASUP ta kuma yi barazanar maka gwamnatin jihar Kano a kotu bisa zargin ta da siyar da filin makarantar ga wasu ɗaiɗaikun mutane.

Mista Zubairu-Chedi ya ce kimanin makonni biyu da suka gabata, malaman makarantar sun gudanar da zanga-zangar lumana a cikin makarantar don su nuna fushinsu.

“Amma, tunda har an fara gini jiya, ba mu da wani zaɓi illa mu ɗauki matakin shar’ia” in ji Mista Zubairu- Chedi.

ASUP ta kuma yi watsi da wani fili da gwamnatin jihar Kano ta ba makarantar a matsayin na maye gurbi, wanda yake a ƙauyen Bagadawa, tsakanin Dawanau zuwa Bichi.

Mista Chedi ya yi mamakin yadda gwamnatin da ta kasa gina fili da yake a zagaye tuntuni a cikin harabar makarantar, za ta iya gina fili fetal mai faɗin hekta 65.73.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan