Ganduje Ya Fi Kowanne Gwamna A Fadin Najeriya Kawo Cigaba – Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

366

A wata ƙididdiga da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar (APC) ke gudanarwa a duk ƙarshen wata domin gano gwamnonin da su ka fi sauran gwamnoni himma da ƙoƙarin samar da cigaba a Jihohin da jam’iyyar ta (APC) ke mulki, a wannan karon ma ƙiyasin ƙididdigar ya tabbatar da Jihar Kano a matsayin Jihar da ta fi dukkan sauran Jihohin ayyukan cigaba a ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.


Watanni biyu ke nan a jere Jihar Kano na zama sahun gaba in da ta ke samun nasarar doke dukkan sauran Jihohin da jam’iyyar (APC) ke mulki, cikin rahoton ƙididdigar a watan Octoba na shekarar 2019 wanda ya bibiyi nasarorin da aka cimma a Jihohin da jam’iyyar (APC) ke mulki.


A takardar albishir da aka aikewa gwamna Ganduje mai ɗauke da sa hannun babban daraktan ƙungiyar gwamnonin, Honarabul Salihu Muhammad Lukman, ta bayyana cewa “dukkan bibiya da nazarin da aka gudanar, a wannan wata Jihar Kano ce ta fi duk sauran Jihohin samar da ɗumbin nasarori a fannoni kimanin guda 19, waɗanda su ka haɗa da samar da ayyukan yi tallafawa matasa wajen dogaro da kai da fannin lafiya da na ilimi da na tsaro da na sufuri da na wutar lantarki da na muhalli da kuma wasanni da sauransu.


Jihar Legas ce ta biyo bayan Jihar Kano da fannoni 18, sai Ekiti mai 17 da Edo mai 13 sai Katsina da Kwara masu 11 kowaccensu sai kuma Jihar Yobe mai 10 da Jigawa mai guda 9, sai Kaduna da Niger da Ogun masu 7 kowaccensu, da kuma Borno da Kebbi mash guda 6 kowaccensu sai kuma Osun da Plateau masu 5 kowaccensu na ƙarshen kuma su ne Jihohin Gombe da Kogi da Nassarawa da Ondo masu guda 4 kowaccensu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan