Wai Yaushe Talakan Kasar Nan Zai Samu Canji A Rayuwarsa Ne?

271

Babu abin da Mallam Talaka yake buƙata tun bayan karɓar ƴancin ƙasar nan daga hannun masu mulkin mallaka a 1960, irin samun gwamnatin da za ta kyautata da inganta rayuwarsa da ta ƴaƴa da jikokinsa. Abubuwan da talaka yake buƙata basu wuce abubuwan da kowa ya sani ake kira da abubuwan more rayuwa ba.

Su fa ababen more rayuwar da ake magana a non, ba wai wasu kayan alatu na a zo a gani ba ne , ba kuma buri talaka yake da shi daga gwamnati na tarin wasu maƙudan kuɗaɗe ko katafarun gine-gine ko manyan filaye ko maka-makan motocin hawa na ƙasaita ba. A’a shi kawai more rayuwa a wajensa bai wuce a samar masa da tsaftataccen ruwan sha ba. Idan kuma ya sami tangarɗar lafiya ya sami asibiti a kusa da shi, ko da irin asibitin ‘sha ka tafi’ ɗin nan ne, domin inganta lafiyarsa da ta iyalinsa. Lallai yana buƙatar a wadata asibitocinsa da likitoci da magunguna a matsayinsa na ɗan ƙasa ba baƙon haure ba.

Talaka yana buƙatar samun ingantacciyar wutar lantarki don haska inda zai samu ya kwanta. Idan ta samu ya ɗan kunna fanka ba wai na’ura mai sanyaya ɗaki irin ta masu ƙasaita ba. Wato dai ya sami ingantacciyar iska domin samun isasshen bacci wanda zafi ko sauro ba zai hana shi yi ba. Da a ce talaka zai sami isasshiyar wutar lantarki da ba a yi masa gorin rashin sana’a ko aikin yi ba.

Wajibi ne a bai wa ƴaƴansa ilmi, alal-aƙalla ilmin firamare har zuwa jami’a (amma ingantacce), wanda idan ya gama karatun zai iya dogaro da kansa ba sai ya zurawa gwamnati ido domin a ba shi aiki ba.
Ba burin talakan ƙasar nan sai kun tura ƴaƴansa ƙasashen turai kamar yadda kuke tura naku suna karatu a can ba.

Talaka yana buƙatar hanya mai kyau wacce zai sami sauƙin karafkiya tsakanin garuruwan maƙwabta ko domin fito da kayan amfanin gona zuwa birni domin cin kasuwa ko don zirga-zirga da yake da ƴancin watayawa a ƙasarsa ta gado.

A ɓangaren tsaro kuwa yana da haƙƙin a kare lafiyarsa, ransa da dukiyarsa, a gida ko akan kowace hanya ta ƙasar nan. Talaka yana ɓukatar ƴancin tafiye-tafiye kan titunan ƙasarsa dare ko rana cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoron ƴan fashi ko garkuwa ko satar mutane ba.

Talaka yana ɓukatar ya sami kayan masarufi cikin rahusa. Yana buƙatar ya biya ƴan buƙatun gabansa a adadin kuɗin da ake biyansa albashi. Ba wai sai ya yi rarar wasu kuɗi don hidimar da ta wuce samunsa ba. Masali talakan da aka kasa fara biya albashin Naira 30,000 a wata, yana fatan idan ya samu kuɗin, to za su biya masa buƙatun wanann wata ba tare da cin bashi ba. Ba tare da ya kai hannunsa ga karɓar rashawa, cin hanci ko satar dukiyar al’umma, domin ciyar da iyalinsa ba.

Wadanan sune mafi ƙarfin buƙatar talakan ƙasar wacce shugabannin ƙasar na da, da na yanzu sojojin su da farar hular su suka gaza biya masa.

Tun samun ƴancin da ake ta zuzutawa wai ƙasar nan ta samu har yau fa talakan bai sami ingantacciyar rayuwar da ta dace da shi ba. Domin har yanzu, kusan shekaru 60 da samun mulkin kai, a wajen talaka dai ba ta canja zani ba. Wato dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Har yanzu talaka bai gani a ƙasa ba.

Sai yaushe ne talaka zai sami canji a wannan tafiya ne. Anya lokaci bai yi ba da talaka zai san ciwon kansa wajen dagewa da nemo mafita akan yadda ake mulkarsa a ƙasar nan?

Wai shin kuwa da a ce har yanzu muna ƙarƙashin mulkin turawan Ingilishi za su bar mu da irin wannan baƙar rayuwar rashin tabbas da shugabannin da suke mulkar mu suke tsunduma mu a ciki kuwa?

✍🏻Ado Abdullahi
Kano-Nijeriya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan