Yadda Ta Wakana Tsakanin Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Da ‘Yan Fim

186

A ranar 27 ga watan Nuwamba, 2019, Ƙungiyar Masana’antar Shirya Fina-finan Hausa ta Arewacin Najeriya, Reshen Jihar Kano, suka kai wa sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Habu Ahmadu Sani ziyara ta musamman a shalkwatar ‘yan sanda dake Bompai a Kano.

A jawabinsa, kwamishinan ya yi alƙawarin aiki tare da al’umma don kawo ƙarshen shaye-shaye, daba da sauran laifuka a jihar kano.

A nasu ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar, Alasan A Ƙwalle ya yi wa kwamishinan alƙawarin yin amfani da sana’arsu don ganin sun ja hankalin matasa domin barin shaye-shaye da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Sannan suka miƙa kyaututtuka da dama ga kwamishinan bisa jajircewarsa a kan aiki, aikin sirri, taimako da iya mu’amala da mutane.

Musa Mai Sana’a da Baba Ari sun gabatar da wasan kwaikwayo na faɗakarwa a yayin ziyarar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan