EFCC Za Ta Binciki El-Rufa’i Bisa Ɓatan Biliyan N32 Lokacin Da Yake Minista

199

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ba zai iya hana Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙi Ta’anati, EFCC binciken sa ba.

Mai Shari’a Binta Nyako ta bayyana haka yayinda take yanke hukunci ranar Juma’a a wata ƙara da Gwamna El-Rufa’i ya shigar mai lamba: FHC/ABJ/CS/60/09.

Gwaman, wanda yake neman kotun da ta yi bayani ko a matsayinsa na Ministan Birnin Tarayya, FCT a wancan lokaci ya bi ƙa’idoji da Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC, ta ta amince da su wajen siyar da gidajen Gwamnatin Tarayya tsakanin watan Mayu 2005 zuwa watan Mayun 2007.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa Gwamna El-Rufa’i shi ne wanda ya shigar da ƙarar, yayinda waɗanda ake ƙara na 1 zuwa na 13 suka haɗa da: EFCC, Ministan Abuja, FCDA, AGF, CBN, Oceanic Bank, Access Bank, Intercontinental Bank, Aso Savings and Loans Ltd, Union Homes, Akintola Williams Deloitte da Aminu Ibrahim and Co.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan