Hukumar KAROTA Ku Daina Baro Ta – Danladi Haruna

183

Karota ta samu gagarumar nasara wajen rage cunkuson masu kasa kaya a titi da daidaita sahun ‘yan arufta da kuma samar da kyakkyawan yanayi a harkar sufuri musamman wajen hana haramtattun tashoshin mota da sauransu.

Sai dai duk da nasarorin da hukumar ke samu, har yanzu da sauran rina a kaba wajen shigr gona da iri da kankanba da zakewar dakarunta wajen tursasa mutane. Ta kai ta kawo dakarun karota sun mai da ransu ba a bakin komai ba muddin za su farantawa gwamnati rai. Ya zuwa yanzu dai muna lissafa dakarun karota takwas da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon artabu da direbobi. Watakila ma lissafin ya fi haka idan da za a bincika sosai.

Da dukkan alamu gwamnati na amfani da karota ne kurum domin tara kudaden shiga ba tare da inganta ayyukansu da tunaninsu ba. Hakan yasa kowacce tabargaza ta taso, su ne a sahun gaba, duk wani nau’i na banƙarawa da musgunawa su ne na farko a masu damara da ke kare muradun gwamnati. Ta yiwu suna yin haka ne domin cika umarni da kuma fatan samun awalaja kamar yadda ake lasa musu domin kuwa an ce yawan cinikin da ka jawowa hukumar yawan ladan gaben da za a ba ka.

Ko ma dai menene, akwai ganganci kwarai dangane da yadda hukumar ke ingiza dakarunta suna shiga sharo ba shanu. Wannan ta sa suka zama jami’ai mafiya bakin jini da tir tsakanin al’umma. Da za su tsaya su jajirce kan ainihin manufar da ta samar da hukumar da ba haka ba.

Akwai bukatar gwamnati ta yi karatun ta nutsu yadda dakarun Karota suka zama wadanda suka fi kowa kasada a aikinsu sabanin sauran dakarun da suka fi su dadewa da gogewa da sanin makamar aiki.

Tsohon yayi ne a cire lambar mutum don ya yi ba daidai ba. Ya kamata a samar musu da na’urorin zamani wadanda za su rika daukar hoton masu laifi suna aikawa gaba. Ya dace a sake ba su horo na musamman wajen kiyaye lafiyarsu da yadda ake mu’amala da mutane da sauransu.

Ya dace hukumar karota ta samar da tsarin tattaunawa da jama’a ta kafofin zamani domin jin koke-kokensu da kokarin gyarawa. Kuma a rika tunatar da jama’a kan dokokin hanya na hakika ba na son zuciya ba.

Sannan hukumar ta duba yiwuwar daukar jama’a masu aikin sa kai, wadanda za su taimakawa bunƙasar aikin nata. A baya akwai wannan tsarin wanda ya taimaka sosai wajen tafiyar da aikin sosai, zuwan sabon shugaban hukumar na yanzu sai ya soke shi. An ce wai ana cigaba da duba hanyoyin da za a dawo da shi.

Abu na gaba, hukumar ta samar da wasu jama’a cikin farin kaya, wadanda za su rika zagayawa suna aikawa ofishinsu rahoto kan yadda abubuwa ke tafiya. Wannan zai sa dakaru su daina kazallaha kuma jama’a su rage hanzarin daukar doka a hannu.

Matukar aka ilmantar da dakarun Karota yadda ya kamata, nasarorin da suka samu za su karu, sannan matsalolin da suke haifarwa kansu da al’umma za su ragu. Muna fata Karota za su daidaita sahu su daina Baro wa kansu halaka, al’umma kuma za su yi karatun ta nutsu su daina yi musu kallon biyu ahu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan