Mata 68,000 Ke Mutuwa Duk Shekara A Najeriya A Wajen Haihuwa- Rotary International

197

Shugaban Shirin Tsarin Iyali na Ƙasa na ƙungiyar Rotary International Project, Farfesa Dolapo Lufadeju, ya ce Najeriya tana rasa mata 68,000 duk shekara sakamakon juna biyu da wahalhalun haihuwa.

Mista Lufadeju ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin Kamfen Shirin Tsarin Iyali na Ƙasa na Rotary International a Ibadan.

Ya ce wannan alƙaluma suna wakiltar kaso 23 cikin ɗari na yawan mace-mace da ake samu a duniya sakamakon juna biyu da wahalhalun haihuwa.

“Wannan yana nuna cewa a duk cikin mata biyar dake mutuwa sakamakon juna biyu da wahalhalun haihuwa, ɗaya ‘yar Najeriya ce, kuma wannan abu ne mai ban tsoro, kuma Rotary International ta damu.

“Rotary International ta kasance wata ƙungiya da take da ‘yan-sa-kai don iya samun damar wayar da kai a ƙauyuka, za ta tattauna da al’ummomi don bada horo da sauransu don rage mutuwa yayin haihuwa.

“Mun zo Kudu Maso Yamma ne don yin taron tattaunawa mu tattara masu ruwa da tsaki wuri guda don shirya tare da yin dabaru bisa matakan da za a ɗauka a shekarau uku masu zuwa don a rage yawan mace-mace yayin haihuwa.

Mista Lufadeju ya ce Rotary International tana ƙawance da Ƙungiyar Likitoci Masana Cututtukan Mata da Masu Kula da Masu Jegu ta Najeriya, SOGON da Ma’aikatar Lafiya don cimma manufarta.

“Za mu ƙara azama da dagewa kuma da matakin Rotary, za mu kawo sabbin matakai tare da kawo mafita ga wannan ƙalubale.

“Za mu wayar da kai a ƙauyuka ta hanyar haɗa kai da masu riƙe da sarautun gargajiya, shugabannin siyasa, shugabannin addini da kuma likitoci da sauransu.

“Burinmu shi ne rage yawan mace-mace lokacin haihuwa, kuma ya kamata kowa ya san cewa abin ya dame mu”, in ji Mista Lufadeju.

Olugbemiga Olowu, Shugaban Shirin na Kudu Maso Yammacin Najeriya da Shugaban SOGON na jihar Ekiti, Dakta Adebayo Adeniyi, a jawabansu daban-daban, sun ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an aiwatar da shirin tsarin iyali yadda ya kamata.

A ta bakin mutanen biyu, bayanan da ake da su sun nuna cewa Najeriya tana bada ‘yar kulawa kaɗan ga shirin tsarin iyali, abinda Rotary za ta tunkara

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan