Home / Labarai / Kuskuren Da Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Mata Ke Yi Wajen Gudanar Da Ayyukansu – Jiddah Gaya

Kuskuren Da Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Mata Ke Yi Wajen Gudanar Da Ayyukansu – Jiddah Gaya

Ƙungiyoyin Fafutukar Ƙwato ‘Yancin Mata sun fara gwagwarmayar neman ’yanci tun a cikin ƙarni na 19, lokacin da su ka fara bayyana neman ’yancinsu a karo na farko a bainar jama’a a birnin Paris da ke Faransa, wato a lokacin da ake taron duniya a kan hakkin ɗan Adam, sai dai duk da haka mata a Turai ba su samu ’yancin yin walwala daga mazansu ba har sai lokacin da tattalin arziƙin Turai ya fara tumbatsa.

Tun daga wancan lokacin a ke samun ɓullar ƙungiyoyi masu rajin kare wani cin zarafi ko wani ƙalubale da mata su ke fuskanta, wanda a mafi yawan lokuta ƙungiyoyin matan su kan yi taron lakca ko wani gangami a kan manufar da su ke son cimma.

Bugu da da ƙari, mafi yawan waɗannan kungiyoyin masu rajin kare haƙƙin mata ko kuma ƙwato musu ‘yanci da su ke rawar gaban hantsi a jihohin Arewacin Najeriya, da mafi yawan mambobin waɗannan kungiyoyi ba su da masaniya ko ilimi a kan abin da su ke kwarmato a kai. Haka kuma ba sa bin salon da ya dace da addini, da al’ adar mutanen da su ke yin abin don su.

Wata babbar matsalar kuma da take kawo tarnaƙi ga ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam da nemar wa wanda aka zalunta haƙƙinsa (musamman mata) ita ce, rashin gina/kafa ƙungiyoyin a kan doran al’adu, aƙidu da kuma yanayin al’ummar da su ke domin su.

Kowa ya sani a ƙasar nan ana fama da matsalolin rayuwa musamman a yankin Arewacin ƙasar nan, wanda kusan kullum cikin kokawa da tattaunawa a kansu muke. Wannan ta sa wanzuwar ƙungiyoyin da dama a cikin al’umma domin dai jagorantar su musamman wajen kai kokensu ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakai, a wasu lokutan kuma su kan yi nasu ƙoƙarin a ƙungiyance wajen magance wasu matsaloli, wanda hakan abu ne mai kyau kuma abin a yaba ne.

Amma a ina gizo ya ke saƙar? Da yawa daga cikin masu fafutukar ko tafiyar da ƙungiyoyin nan ba sa la’akari da al’ummar da su ke yin wannan aiki domin su, da yawa na gudanar da harkokinsu bisa aƙidun da shi wanda suke ƙoƙarin yin wannan abun dominsa zai iya yin Allah-wadai da su, ko da kuwa suna tunanin sun yi ne domin kawo gyara amma saboda kauce al’adar mutanen sai hakan ya jawo rincaɓewar al’amura, ka ga kenan garin neman gyara ka haifar wa da kanka matsala.

Akwai buƙatar duk wani mai gudanar da ƙungiya ya tsaya ya nutsu sosai ya san waɗanne irin mutane zai yi wa aiki, mene ne al’adunsu, ya za su fuskanci saƙon da kake shirin isar wa gare su, wace irin shiga ya kamata ka tunkare su da ita a matsayinka na mai ƙoƙarin magance musu matsaloli, kuma ka kasance mai karɓar gyara yayin da ka aikata ba daidai ba, “Matar na tuba an ce ba ta rasa miji”.


Waɗannan kadan kenan daga cikin abubuwan da ya kamata a dinga la’akari da su, ba wai kawai ka zo da wasu aƙidun da sun ci karo da na al’ummar da ka ke kwarmato domin su ba, kuma a yi zaton za a kawo gyara.

Ga matan da suke cikin ƙungiyoyin irin wannan, ya kamata ku sani mace halittace da take da samatsi abu ƙalilan zai iya haifar wa rayuwarta matsala, ki sani cewa ke ɗin kamar tangaran ce ko ƙwai, ɗan ƙwarzane kaɗan zai iya yi miki lahani. Haka ki ke, abu ƙalilan zai iya jefa rayuwarki cikin hatsari ko da-na-sani.

Saboda haka idan har kana son kawo gyara ko sauyi to ka kawoshi ta hanyar da ta dace, ma’ana ta hanyar bin tarihi da al’adun al’ummar domin ta hakan ne za ka kawo gyaran da kake ƙoƙarin kawowa cikin sauƙi.

Jiddah Gaya Ta Rubuto Daga Kano

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Micheal Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya cika shekaru 85 da haihuwa

A yau Litinin 10 ga watan Mayun shekarar 2021 mutumin nan da ya zama tutar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *