Masarautar Kano: ‘Yan Santsi Da Gidan Dabo – Fatihu Mustapha

414

“Wani cigaba bai taba zuwa arewa ba, sai samarin zamanin sunyi amfani da shi, sun ci mutincin dattawan cikinsu….”

(Farfesa Murray Last)

Manufata a wannan sako shine, in kalli alakar siyasa da tarihi, dake tsakanin gidan malam Ibrahim Dabo, da gungun yan siyasa masu tsattsauran raayin kawo sauyi, wanda aka fi sani da “Yan Santsi” a Tarihin siyasar Kano. Ina son in kalli abin ta bangaren tarihin siyasa da kuma yadda alakar tasu kan haifar da rikici a duk lokacin da wadannan bangarori biyu na siyasar Kano suka yi juna shigar gizagizai. Zan kuma nuna cewa, dama can babban burin duk wani dan santsi shine ya ga bayan masarautar Kano.

Koda yake Sullubawa sun zo Kano tun lokacin jihadi, amma masana sun bayyana malam Ibrahim Dabo na cikin manyan Fulani da suka zo Kano bayan an gama jihadi, ciki kuwa har da gidan limamin Kano Malam Muhammad Zara da wasu daga ciki. Mum dai san wadanda suka jagoranci jihadi a Kano sun hada da: Malam Jibir, Malam Dangabuwi, Malam Bakatsine, Mal Sulaimanu, Alkali Usman al Hausawi, Malam Goshi, Dabon Dambazau da kuma Chiroman Kano Danmama dan Sarkin Kano Sharefa.

Irin zaman doya da manja da akayi a tsakanin manyan qabilun Fulani da suka yi jihadi, ya sanya Malam Sulaimanu ya nemi alfarmar bayan ransa, yana rokon a nada daya daga cikin ukun nan: kodai Malam Ibrahim Dabo, ko Alkali Usman al Hausawi ko Chiroman Kano Danmama. Inda Allah cikin ikonsa duk da yake akwai manyan Fulani da suka rayu bayan Sarkin Sulaimanu, amma aka nada Dabon Kanwa a matsayin Sarkin Kano.

Wata baiwa da Allah yayi ma Sarkin Kano Dabo ita ce, gwanintar jagoranci da siyasar alamurran mutane. Babban matakin da Dabo ya dauka na hade kan alumma da kuma kawo tsarin mulki da zai dore a Kano shine ya zama maslahar alumma, inda ya kafa majalisar nan ta nadin sarki bayan ya rasu, ya debi manyan gidajen Fulani gudu hudu ya sanya su a wannan majalisar, wadanda suka hada da: Gidan Makaman Kano Malam Bakatsine, Gidan Sarkin bai Malam Dabon Dambazau da gidan, Madakin Kano Malam Jibir, da kuma gidan Sullubawan Tuta, wadanda yanuwansa ne na kutan. Wannan dabarar siyasa ta nuna daga yanzu, bawani gidan Fulani da zasu Kara neman sarautar Kano in ba ahlinsa ba, balle ma azo ana wani fitina akan neman sarauta. Domin dai baka zama mai zaben sarki ba, sannan kuma ka zabi kanka. Uku daga cikin wadannan da na lissafa a sama, su ake cewa: “uku kun fi Sarki”, saboda su suke nada Sarkin. Duk wanda yayi sallama yayi sallama zai ga sarki, to kome Sarkin yake, dole ya fito. Tun daga wannan lokaci, tsarin masarautar Kano yake a haka, kuma tun a wancan lokaci sauran kabilun Fulani suka yadda da hakan, duk da yake an samu wasu yan matsaloli nan da can, a farkon fara kafa majalisar, wadda ta kai ga cire Makaman Kano Mandinko, aka nada kaninsa Makama Sani.

Zuwan Turawa ya zo da sabbin sauye sauye, da suka taba matsayin siyasa na sarakunan gargajiya. Daya daga cikinsu kuwa shine: tsarin siyasar Zamani, inda aka bada dama aka kafa kungiyar siyasa domin tsayawa takara, dan zama danmajalisa, ko zama firimiya, ko prime minister. Tun a karshen shekarun 1950s aka fara yunkurin kafa kungiyoyin siyasa a arewacin Nigeria, bayan wasu yan arewa irinsu: Malam Abba Jiddum, Raji Abdalla, da su Malam Saadu Zungur sun ga irin wariyar da ake nuna musu a kungiyoyin siyasu na Kudancin Nigeria, musamman a kungiyar siyasar nan ta NCNC ta Dr Nmandi Azikwe. Wannan ce ta sanya suka dawo gida domin su kafa tasu siyasar ta yan arewa, inda aka fara kafa Jamiyyar Mutanen Arewa Ayau. Wannan kungiyar ita ce ta fashe ta zama NPC karkashin jagorancin likita: Russel Barau Dikko da kuma NEPU karkashin Jagorancin Malam Abba Danmaikwaru. Inda daga baya Sardauna Ahmad Ibrahim Raba (wanda aka fi sani da Sir Ahmadu Bello), da kuma Malam Aminu Sudawa (wanda aka fi sani da Malam Aminu Kano) suka karbe jagorancinsu.

Kungiyar siyasa ta NEPU ita ce kungiyar da tafi daukar hankalin mutanen Kano, musamman saboda aqidar kawo sauyi da take da shi. Malam Magaji Dambatta, na daya daga cikin mutane 8 da suka kafa wannan kungiya, kuma yayi cikakken bayani akan yadda aka kafata a littafin tarihinsa da ya rubuta wato: Pull of Fate. Wannan kungiya ta siyasa ta zo da wata Aqida da ta kira “Yanto alumma daga zaluncin sarakuna da turawan mulki. Sai dai wasu suna kalubalantar wannan Aqida ta NEPU da cewa bata haifar da komai ga arewa ba, illa samar fitsara da rashin kunya gindin zama a kasar Hausa. Wasu ma na da raayin cewa, shine ummulhaba’isin da ya sanya, har lokacin da sojoji suka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966 , kungiyar bata tabuka wani abin kuzo ku gani ba, a zabubbukan da aka gudanar a kasar nan ba.

HAIHUWAR AQIDAR SANTSI
Bayan sojoji sun shafe shekaru kusan 13 suna mulki a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979 suka maida mulki a hannun farar hula. A Kano kamar sauran jihohin kasar nan, jam’iyyu biyar sun shiga takara, kuma jamiyyar PRP ta malam Aminu Kano, mai raayin kawo sauyi ita ce tayi nasara a zaben gwamna da akayi, inda Alhaji Abubakar Rimi na Jamiyyar PRP ya kada abokan takararsa na sauran jamiyyun. PRP dai jamiyyar ce da aka gina ta akan aqidun Tsohuwar NEPU, da nufin karbar mulki ta hanyar dimokaradiya domin a kawo sauyi, wannan Aqida ta ta, ta sanya mata farin jini a wurin yan boko, musamman malaman Jamia, maaikata, Malaman makarantu, kungiyoyin kwadago da matasa da kuma talakawa. Sai dai kash! Wannan hadaka bata je ko ina ba, sai aka fara samun rikicin cikin gida tsakanin tsoffin yan siyasa da suka gangaro daga NEPU zuwa PRP da kuma Yan Boko da mafi yawansu sun fara siyasa ne zamanin jamhuriya ta biyu. Akan haka wannan jamiyya ta dare gida biyu, tsakanin masu goyon bayan shugaban ta na kasa baki daya: Malam Aminu Kano, da kuma daya bangaren da ke karkashin gwamnan Kano: Alhaji Muhammad Abubakar Rimi.

Malam Aminu ya kalli wannan yunkuri na bangaren gwamna a matsayin wani tawaye , ko kuma halin nan na kaza ci ki goge bakinki, a wata lacca tasa, yayi kashedi ga mabiya da su yi hattara kar su yadda wannan santsi ya kwashe su su abka wancan bangare na Gwamna, wannan shine asalin da aka fara kiran wannan bangare na PRP da sunan santsi. Kamar yadda shima daya bangaren, Alhaji Sabo Bakinzuwo ya sanya masa sunan Tabo.

Farkon Rikici

Baya ga rikicin gwamnoni tara (9), wani babban dalilin da ya jawo wannan rikicin cikin gida tsakanin malam Aminu da halifansa: Gwamna Rimi shine, matsayin gwamnatin Kano akan masarautar Kano. A wannan lokaci, gwamnatin Kano ta dau matakin ba sani ba sabo akan masarautar Kano, baya ga rarrabawa masarautar da gwamnan yayi zuwa masarautun Kano, Gaya da Rano, ya kuma nuna aniyarsa ta lallai sai ya kwabe Sarkin Kano Ado Bayero, inda ya fara da aika masa da takardar tuhuma. Malam Aminu na cikin wadanda suka kira wannan yunkuri da hauka. Kuma suka kalubalanci wannan yunkuri na gwamnatin Kano. Hasali ma dai, shi kansa Sarkin Kano mutum na farko da ya fara sanarwa da wannan tuhuma, shine Malam Aminu Kano. Karshe dai wannan rikicin shine ya janyo Tashin Tashinar Goma ga watan July wato July 10 Rampage, wacce ta janyo asarar dukiyoyi da rayuka a Kano, ciki kuwa har da babban mai baiwa gwamna shawara akan harkokin siyasa : Dr Bala Muhammad. Daya daga cikin tsauraran matakan da gwamnatin Rimi ta dauka akan masarautar Kano shine; hana hawan sallah, duk kuwa da gwamnatin ta amince da ayi a wasu masarautun, har ma gwamnan kanyi tawaga ya tafi Gumel kallon hawa.

SANTSI DA MASARAUTAR KANO A YAU
Tun bayan da aka yi juyin mulki na shekarar 1983, bawani mai aqidar santsi da ya kara samun damar zama gwamna sai a zaben 2015, in da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbin ubandakinsa a siyasa wato Dr Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi kuma ya fito daga bangaren tabo.

Kafin hawan nasa gwamna, Ganduje a matsayinsa na mataimakin gwamna, yayi uwa yayi makarbiya, a rikicin da ya kunno kai tsakanin Masarautar da gwamnatin Kano, akan rikicin nadin wazirin Kano, ya fito fili ya sanarwa da yan jarida cewa a shirye suke su cire Sarkin Kano Ado , in har ba zai yadda yabi umarnin gwmanti ba. Da bakin cikin wadannan bakaken maganganu maimartaba Sarkin Kano Ado ya bar duniya.

Wanda ya gaji Sarkin Kano Ado shi ne : Malam Lamido Sunusi Lamido. Ya hau karagar mulki ba da jimawa ba aka yi zaben 2015, inda Ganduje ya lashe zaben. Koda yake akwai banbancin raayi a yadda Sarkin Kano Ado ya ke muamala da yan siyasa, da yadda Sarkin Kano Sunusi yake yi. Amma dai kusan wannan tsohon mikin na yan santsi yana nan a zuciyarsu. Wannan miki kuwa shine; na ganin sun cika burin limaminsu na ragewa masarautar Kano karfin iko ta hanyar yi mata kishiyoyi, ko kuma kawar da Sarkin Kano su nada nasu dan barandar.

Rikici ya fara kunno kai ne, tun bayan da Sarkin Kano Sunusi yayi abin nan da ake kira da gyara kayanka, akan shirin gwamnatin jiha na shimfida layin jirgin kasa a cikin birnin Kano. Inda Sarkin ya bayyana shi a raayinsa , da a ciwo bashi a yi wannan, gara ayi amfani da kudin a gyara makarantun da asibitoci da masanaantu. Na biyu shine taron habaka tattalin arzikin Kano da aka gabatar a jamiar Bayero, inda aka gayyaci kowa Amma baa gayyaci gwamnati ba. Wannan ma ya kara hassala gwamnati , taga ya zama wajibi ta dau matakin da zai rage karfin masarautar Kano.

Matakin farko shine: yin amfani da majalisar dokokin jiha a kafa dokar da zata bada damar kafa sabbin masarautu, inda aka kafa masarautun Bichi, Karaye, Rano da Gaya. Kamar dai a yau burin yan santsi ya cika, sun sake komawa gidansu na jiya. Sai dai a wannan karon, sunyi nasarar yin abubuwan da shi limamin nasu bai yi ba: yin dokar kafa masarautun, da kuma yin nasarar darewar gidan Dabo, tsakanin Bichi da Kano. Inda aka dauko daya daga cikin yayan Sarkin Kano Ado akayi masa Sarkin Bichi, wanda hakan ya janyo rabuwar Kai da lalacewar zumunci a tsakanin ahlin gidan sarautar.

Wani abu kuma shine, yadda gwamnatin ke nuna ita bata san wani sarki a jihar Kano ba, in ba Sarkin Bichi, duk kuwa da cewar, har a yanzu, hakimai da dama da talakawa sunyi wa wannan sabin sarakuna bore. Kusan dai ina zaton, tsoron wakiar 10 ga watan July ce, na kar ta kara faruwa ta sanya Gwamnati ta kasa cimma burinta na cire Sarkin Kano ta nada wani.

Allahu a’lamu

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan