Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywood, wato Teema Makamashi (Jakadiyar FKD) ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa jaruman masana’antar Kannywood basu da tarbiyya.
Makamashi, ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jarumar tayi da gidan rediyon Freedom dake Kano, ta bayyana cewa “Mu muke da tarbiya, saboda mu muke bada gudummuwa wajen gina tarbiyar ‘ya’yan mutane, na san wadanda suke yawace-yawacen sata, da karuwanci amma sanadiyar wani film da suka kalla sun daina”.
Teema Makamashi ta kara da cewa mafi yawa bakin haure a masana’antar ne ke bata musu suna, amma su ‘yan film mutane ne masu daraja da tarbiyya.
Turawa Abokai