Yawan Amfani Da Wayar Salula Na Toshe Basira – Bincike

675

Wani bincike da likitocin kwakwalwa suka gudanar ya ce kusan kashi daya bisa uku na matasa sun shaku da wayoyin zamani har ma abin ke neman zame musu kamar ba za su iya rayuwa sai da waya.

Binciken da kwalejin Kings a birnin London ta yi ya ce mutane na shiga yanayin damuwa a duk lokacin da aka ce ba su tare da wayoyinsu.

Rahoton ya ce matasa ba sa iya takaita lokacin da suke shafewa suna dannar waya.

Binciken ya kuma ce irin wannan shakuwa da wayoyin zamani na iya shafar lafiyar kwakwalwar mutum.

Shi dai binciken, wanda aka wallafa a mujallar BMC Psychiatry, ya yi nazari kan wasu bincike har 41 da aka yi kan matasa 42,000 game da matsalar amfani da wayoyin zamani.

Binciken ya gano cewa kashi 23 cikin dari na matasan, waya ta zame musu kamar abin da ba za su iya rayuwa ba sai da ita – irin halin da suke shiga idan ba sa iya amfani da wayarsu da kuma rashin iya kayyade lokacin da suke shafewa akan wayoyin har ta kai ga hakan na zama hadari ga wasu harkokinsu.

Irin wannan dabi’a ta shakuwa da waya ana iya danganta ta da sauran matsaloli, kamar yadda binciken ya bayyana, kamar gajiya, da damuwa da rashin bacci da kuma rashin yin kokari a makaranta.

Daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton, Nicola Kalk daga cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa a kwalejin Kings da ke birnin London, ya ce, “wayoyin zamani sun samu wajen zama kuma akwai bukatar a fahimci irin matsalolin da ke tattare da amfani da wayoyin.”

A cewar Dr Kalk, ”ba mu sani ba ko wayar zamanin ce ta ke da shiga ran mai ita ko kuma manhajojin da mutane suke amfani da su.

“Duk da haka, akwai bukatar a wayar wa da mutane kai game da yadda yara da matasa ke amfani da wayoyin zamani da kuma bukatar iyaye su san iya lokacin da ‘ya’yansu suke shafewa akan wayoyinsu.”

Ita ma Samantha Sohn, ta ce shakuwa da waya na “iya shafar lafiyar kwakwalwa da kuma harkokin yau da kullum, akwai bukatar a zurfafa bincike kan matsalolin da ke tattare da yin amfani da wayoyin zamani”.

Sai dai Amy Orben, wata malama a sashen kimiyyar kwakwalwa a jami’ar Cambridge, ta ja hankali game da tunanin cewa akwai wata alaka tsakanin yawan amfani da wayoyin zamani da kuma matsalolin damuwa’.’

A cewarta, a baya, an nuna cewa illar yin amfani da wayoyin zamani ba wai daga wayoyin ba ne kadai, yanayin mutum ma kan iya yanke yawan lokacin da mutum zai shafe akan waya”.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan