Dino Melaye Ya Sha Kaye A Zaɓen Sanatan Kogi Ta Yamma

181

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana Smart Adeyemi, ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen Sanatan Kogi ta Yamma a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ya kayar da Dino Melaye na jam’iyyar PDP.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Asabar da daddare a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe a Kogi, Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen, Farfesa Olajide Lawal, ya bayyana cewa Mista Adeyemi ya samu jimillar ƙuri’u 88,373, inda ya doke Mista Melaye, wanda ya samu ƙuri’u 62,133.

Rufus Aiyenigba na jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, ya zo na uku da ƙur’iu 659, John Olabode na African Democratic Party, ADC, ya samu ƙuri’u 262, yayinda Adeyemi Taiwo na New Nigeria Progressive Party, NEPP, ya samu ƙuri’u 119.

Wannan zaɓe ya zo ne bayan zaɓen zagaye na biyu da INEC ta gudanar ranar 16 ga Nuwamba ya gaza samar da wanda ya yi nasara.

Rahotonni sun bayyana cewa wancan zaɓe a cike yake da tashin hankali da sauran laifukan zaɓe.

Koda yake sakamakon zaɓen na biyu ya nuna Mista Adeyemi na kan gaba da ƙuri’u 80,118, inda ya doke Mista Melaye wanda ya samu ƙuri’u 59,548, Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen ya ce dokar zaɓe ta yi masa tarnaƙi ta hana shi bayyana wanda ya yi nasara.

Ya yi bayanin cewa ratar ƙuri’u 20,570 dake tsakanin ‘yan takarar biyu ba ta kai yawan ƙuri’un da aka soke a mazaɓu 53 da aka yi rijistar zaɓe ba.

Biyo bayan nasarar ɗan takarar na APC, Mista Adeyemi a wannan zaɓe, idan ya karɓi Takardar Shaidar Lashe Zaɓe zai maye gurbin Mista Melaye a matsayin Sanata da zai wakilci Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai.

Sake sabon zaɓen da INEC ta yi a mazaɓar ya biyo bayan umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja, wadda ta yi watsi da ƙarar Mista Melaye, wanda yake ƙalubalantar soke zaɓensa na ranar 23 ga Fabrairu da wata kotu ta yi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan