Wata Jami’a Ta Baiwa Malam Shekarau Digirin Girmamawa Akan Fannin Ilimi

114

Jami’ar Ritman University wacce mai zaman kanta ce a jihar Akwa Ibom ce ta baiwa Sanata Mallam Ibrahim Shekarau digirin girmamawa (Dr.) Honoris Causa a fannin ilimi da falsafa.

An baiwa Malam Shekarau wannan digirin girmamawa ne saboda gudunmawar da ya bayar a harkar ilimi, da kuma kasancewar a shekarar 2015 a zamanin da yake ministan ilimi aka baiwa ita Ritman University lasisi.

Wannan dai shi ne karo na uku da wata jami’a ta baiwa Shekarau babban digiri na girmamawa, bayan da jami’ar Najeriya ta Nsukka da ke jihar Anambra da kuma jami’ar Al Hikma ta Ilorin a jihar Kwara su ka ba shi digirin girmamawar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan