Gwamna Ganduje Ya Sa Ke Gabatar Da Kudirin Kafa Sabbin Masarautu 4 Ga Zauren Majalisa

253

Makwanni biyu da hukuncin wata babbar kotun jihar Kano na soke sabbin Masarautun da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira, gwamnatin jihar Kano ta sa ke gabatar da sabon kudiri ga zauren majalisar dokokin jihar Kano domin sake kafa wadannan masarautu.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishanan yada labaran jihar Kano Mohammaed Garba ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa majalisar zartarwan jihar ta yanke shawarar sa ke gabatar da kudirin ne a zamanta da ta yi jiya lahadi.
Sababbin masarautun da aka gabatar su ne Rano, Gaya, Bichi da Karaye.


Mohammed Garba ya bayyana cewa majalisar zartarwan ta tattauna lamarin kafa sabbin masarautun da aka kwashe shekaru goma ana bukata domin samar da cigaba da alfanu ga al’ummarsu.


Ya ce an samar da wasu daga cikin sabbin masarautun kafin Kano amma an gaza dawo da su.


Idan za’a iya tunawa dai Makwanni biyu da su ka gabata wata babbar kotu a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’Abba ta so ke karin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro.

A lokacin yanke hukunci kotun ta ce majalisar dokokin jihar Kano ta yi karantsaye ga tanadin sashi na 101 na kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, wanda ya ba ‘yan majalisar damar zartar da doka.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan