Kadiri Ikhana Zaikoma Asibiti Agobe Talata

226

Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafan mata ta Super Falcons harma da Enyimba International na garin Aba wato Kadiri Ikhana zaikoma asibiti agobe Talata domin cigaba da duba lafiyarsa.

Akarshen makonnan dai aka sallameshi daga asibitin Alliance na babban birnin tarayya Abuja inda akayimasa aiki a kutirinsa karo na biyu.

Mahukuntan asibitinne dai suka bayar da sanarwar cewa yakoma ranar Talata domin sake duba lafiyar tasa.

Ikhana dai ya taba jagorantar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta lashe gasar zakarun nahiyar Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan