Ana zargin wani jami’in ɗan sanda a ƙaramar hukumar Owo ta jihar Ondo ya buɗe wuta a kan wani direba bisa ƙin tsayawa ya bada nagoro a wani wajen binciken ababen hawa, a cewar rahotan jaridar The Cable.
Direban da har yanzu ba a gano ba, ana sa ran an harbe shi da misalin ƙarfe 1 na ranar Litinin yayinda yake kan hanyar kai wasu kaya zuwa Abuja.
A cewar wani shaida, jami’in ɗan sandan da yake a wajen binciken ababen hawa a Uso ya tsayar da direban, sannan ya bayyana masa abinda yake buƙata, amma direban ya ƙi ya bayar, inda ya daga a kan cewa takardun motarsa cikakku ne.
Shaidar ya ce: “Ɗan sandan ya tsayar da direban kuma ya tsaya. Bayan nan sai suka buƙaci ya ba su kuɗi amma ya ƙi, inda ya daga kan cewa dukkan takardunsa cikakku ne. Abin dai ya zama cacar baki. Cacar bakin ta yi sanadiyyar harbe direban nan take.
Da yake mayar da martani ga faruwar al’amarin, mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ondo, Femi Joseph, ya siffanta taɓargazar ɗan sandan a matsayin aikin dabbanci.
Ya ce tuni Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar ya bada umarnin a yi ƙwaƙƙwaran bincike a kan al’amarin.
“Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ondo tana alhinin mummunan al’amarin da ya afku wanda ya haifar da mutuwar wani direban motar ɗaukar kaya da har yanzu ba a gano shi ba a yau 2/12/2019”, in ji Mista Joseph.
“Ana zargin ɗaya daga cikin jami’anmu wanda yake bakin aiki tare da sauran jami’anmu shi ya harbe direban har lahira da misalin ƙarfe 1:00 na rana a Uso dake Owo.
“Rundunar tana Allah-wadai da wannan aiki na dabbanci da kuma kisan gilla gaba ɗaya. Yayinda muke taya iyalan mamacin alhini, muna so mu ce abinda wannan jami’i ya aikata ba ya wakiltar abinda Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa ta tsaya a kai.
“Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ondo suna girmama rayuwa da mutuncin al’umma kamar yadda aka gindaya a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
“Sakamakon haka, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ondo ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike, shi kuma jami’in zai fuskanci fushin hukuma.
“A karo na biyu, muna ƙara neman afuwa bisa irin rashin jin daɗi da kiɗimewa da wannan al’amari zai iya jawo wa ko wane ne” in ji shi.
[…] Muƙalar Da Ta GabataƊan Sanda Ya Harbe Direba Har Lahira A Ondo Saboda Ya Ƙi Bada Nagoro […]