An Hana ‘Yan Najeriya 1,044 Fita Zuwa Ƙasashen Waje

211

Gwamnatin Najeriya ta hana a ƙalla ‘yan Najeriya 1,044 daga fita zuwa ƙasashen waje a 2018, a cewar jaridar The Punch.

Jaridar ta ce ba ba a gano dalilin da yasa gwamnati ta ɗauki matakin hana su tafiye-tafiyen ba, amma ana zaton wata ƙila mutanen suna kan jerin sunayen da jami’an tsaro ke nema sakamakon aikata laifuka daban-daban.

Matakin da aka aiwatar ƙarƙashin ikon Hukumar Kula da Shige da Fice, ya kuma hana baƙi ‘yan ƙasashen waje 22,889 shigowa Najeriya.

A 2017, an hana ‘yan Najeriya 31,672 da ke kan jerin sunayen da jami’an tsaron Hukumar Kula da Shige da Fice ke son kamawa fita zuwa ƙasashen waje.

A cewar The Punch, bayanan farko-farko da aka samo daga Rahotan Shekara-Shekara na NIS, 2018, ya kuma nuna cewa NIS ta bada bizar aiki ta wucin gadi ga ma’aikata ‘yan ƙasashen waje 15,186, ta samu fiye da biliyan N39.

Rahoton ya ƙara nuni da cewa an dawo da ‘yan Najeriya 17,616 gida a bara, yayinda aka dawo da 339 daga ƙasashe daban-daban.

“An samu mutane 33 da suka so tserewa a jiragen ruwa a shekarar”, in hukumar.

A wani ɓangaren kuma, Hukumar Kula da Shige da Fice ta bada fasfo 1,227,158 da kuma takardar izinin zama a ƙasa 63,816 a 2018.

Hukumar ta kuma bada katinan izinin zama na ECOWAS guda 4,466, yayinda ta bada biza 177,168 a ofisoshin jakadancin Najeriya daban-daban.

Kimanin matafiya ‘yan ƙasashen waje 4,529,158 ne suka ƙetara iyakokin ƙasar nan, ƙarin kaso 22 cikin ɗari a kan na 2017.

Bayanin ya nuna kaso 78 cikin ɗari na matafiyan sun zo ne ta jiragen sama, kaso 21 cikin ɗari sun zo ta ƙasa, kaso ɗaya kuma sun zo ta teku.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan