Ba Maganar Buɗe Boda A Halin Yanzu- Buhari

369

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai bada wata rana da za a sake buɗe bakin iyajokin ƙasa na Najeriya ba.

Ya ce rufe bakin iyajokin zai ci gaba har sai abubuwa sun inganta.

Shugaban Ƙasar ya ce amfani da man fetur a gida ya yi ƙasa da kaso 30 cikin ɗari tun da aka rufe bodar.

Garba Shehu, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja cewa Shugaban Ƙasa ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi tawagar Ƙungiyar Dattawan Jihar Katsina a mahaifarsa, wato Daura dake jihar ta Katsina.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatisa ta bada umarnin a rufe bakin iyakar ne don daƙile ɗabi’ar shigo da kaya ba bisa ka’ida ba, musamman shinkafa, kuma kawo yanzu, rufe bodar ya sa ƙasar nan ta ajiye kuɗaɗen shigo da kaya masu taurin yawa.

Ya ce gwamnatin tasa tana ɗaukar wasu matakai don farfaɗo da ɓangaren aikin gona a ƙasar nan.

Shugaban Ƙasar ya yaba da matakin da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadou Youssoufou ya ɗauka, wanda ya haɗa da korar wasu jami’ai da kuma haramta amfani da ƙasar a matsayin ƙasar da ake jibge kayan da aka shigo da su daga Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Shugaba Buhari ya lura da cewa matakan da Nijar ɗin ta ɗauka sun taimaka wa muradun Najeriya.

Ya yadda da irin wahalhalun da garuruwan dake zaune a kan iyakoki ke sha bisa yadda aka hana siyar musu da man fetur kilomita 20 kafin inda boda take, wani mataki da ya kai ga rufe dukkan gidajen man da suke Daura, mahaifarsa.

“Dole a kare manoma, rashin gaskiya ya yi yawa a ƙasar nan. Ba don haka ba, da ba a bada umarnin rufe bodar ba”, in ji shi.

Ya ce hana siyar da man fetur ɗin garuruwan dake bakin boda na ɗan lokaci ne saboda Hukumar Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS tana so ta san ainihin mutanen dake hada-hadar siyar da kayayyaki da waɗanda ake amfani da su don shigo da kaya ba bisa ka’ida ba.

Shugaba Buhari ya faɗa wa tawagar cewa zai ci gaba da ɓullo da shirye-shiryen kakkaɓe talauci da kuma gyare-gyare a ɓangaren aikin gona da kiwon dabbobi da gwamnatinsa ta fara tuni, tunda an kammala zaɓe kuma an kafa gwamnati.

Ya bayyana cewa gyare-gyaren, musamman waɗanda ke da alaƙa da tsugunar da manoma za su ɗauki lokacin kafin a kammala.

Ya ce buƙatarsa ta aiwatar da gyare-gyare a aikin gona yadda ya kamata ita ta sa ya zaɓi manoma da aka gwada su a matsayin ministocinsa na da da na yanzu.

Da yake jawabi tunda farko, wakilin Shugaban Ƙungiyar Dattawan, Alhaji Aliyu Saulawa, ya yaba wa Shugaban Ƙasa da Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina bisa kawo ƙarshen aikace-aikacen mahara, masu garkuwa da mutane da ɓarayin shanu.

Amma ya kawo jerin buƙatu waɗsnda suka haɗa da kira ga gwamnati don bada tallafi na musamman ga waɗanda hare-hare suka shafa, kammala gina tashar wutar lantarki mai megawat 10 a jihar, kafa Hukumar Raya Arewa Maso Gabas da kuma kafa Rugage.

A ta bakinsa, makiyaya suna buƙatar Rugage.

Ƙungiyar Dattawan ta kuma gabatar da buƙatar samun ayyukan raya ƙasa a jihar, ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da shirye-shiryen kakkaɓe talauci a jihar.

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin duba waɗannan buƙatu.

Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa shi fa mazaɓarsa ita ce Najeriya gaba ɗaya, ya kuma ce zai yi wa kowa adalci, waɗanda suka zaɓe shi da ma waɗanda ba su zaɓe shi ba.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. yakamata shugaban ƙasa buhari yasauka domin gazawarsa tabayyana afili garashin tsaro garashin kulawa da rasa rayukan jama’a kullum,ga barazana ga talaka maikuɗi nacin karensa ba babbaka aƙarshe manyan ƙasa nata wawurar kuɗin gwamnati amma shiru kakeji.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan