Ko Meyasa Mutane Basa Korafi Dangane da Ballon d ‘Or Akan Messi?

173

Tun bayan bikin bayar da gasar Ballon d’Or da akayi a kasar France bakin mutane tsit yayi akan cewar bai cancanta ba idan aka kwatanta da korafin da mutane sukeyi lokacin da aka bashi kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya.

Mutane dai a wancan karon sunsha yin surutu akan cewa Van Dajk na Liverpool ne ya cancanta.

Ita dai wannan kyautar Messi ya lashe sau 6 kenan inda yafi kowanne dan wasa kashewa.

Wannan kyauta tun daga 2008 Christiano Ronaldo da Measi suke yin bani na baka wanda sai a kakar wasan data gabata ne Luka Modrić ya lashe.

Rabon da Messi ya lashe kyautar tun a 2015 lokacin da yadauka karo na 5.

Ga dalilan da sukasa Messi ya lashe wannan kyauta:

  1. yaci kwallaye 54 akalar wasan data gabata.
  2. Ya taimaka anci kwallaye 23.
  3. Yafi kowa jefa kwallaye agasar zakarun nahiyar turai.
  4. Yafi kowa jefa kwallaye agasar Laliga.
  5. Yafi kowa taimakawa wajen cin kwallaye a gasar Laliga.
  6. Shine dan wasan da yafi kowa kokari a gasar Laliga.
  7. Shine dan wasan gaba da yafi kowa kokari anahiyar turai.
  8. Ya lashe gasar Laliga.
  9. Ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya.
  10. Shine dan wasan da yafi kowa kwazo agasar Laliga.

Haka avangaren mata ‘yar wasa Rapinoe ce ta lashe kyautar wato ‘yar kasar Amurka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan