Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gargadi Ganduje Akan Sabbin Masarautu

143

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Dahiru Bauchi ya roki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje cewa ya janye aniyyarsa ta dawo da sabbin masarautun jihar.

Malamin ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da ya aiko wa BBC Hausa.A cikin sakon malamin ya ce: ”Ina rokon Ganduje don Allah, don Annabi ya bar batun (kirkiro sabbin masarautu) kamar yadda kotu ta soke su.”Ko a kwanakin baya sai da malamin ya nuna rashin jin dadinsa bayan an kafa masarautun a kwanakin baya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce “ina jawo hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa, to ya hakura tun da ( kotu ta mayar) da Kano kamar yadda take shekara dubu da wani abu.”

Tun da farko Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aika wa majalisar dokokin jihar Kano sabon kuduri akan sabbin masarautu Kano.

Malamin ya ce “Ganduje ya kammala aikinsa cikin zaman lafiya, ya fi kan ya kammala ana tsine masa.”Ya kuma ce ”taba fadar Kano, taba mu ne gaba daya ‘yan Tijjaniyya ne da masoyanmu.”
Malamin dai ya ce da fatan gwamnan zai ji shawarar da ya ba shi kuma ya bar Kano ta zauna lafiya kamar yadda ya same ta.

A ranar Litinin ne Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aika da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka’ida ba. Rahotan BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan