‘Yan Najeriya Sun Fara Cin Moriyar Tafiye-Tafiyen Buhari- Hadimin Shugaban Ƙasa

319

Ajuri Ngelale, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari Kan Al’amuran Aikin Gwamnati, ya ce ‘yan Najeriya sun fara amfana da tafiye-tafiyen da Shugaban Ƙasa ke yi zuwa ƙasashen waje.

Idan dai za a iya tunawa, ana caccakar Shugaban Ƙasar bisa zargin sa da yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare.

Sai dai Mista Ngelale, a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Abuja ya ce: “Waɗannan tafiye-tafiye suna da tarin alfanu”.

Ya bayyana Shugaban Ƙasa a matsayin shugaban da ƙasashen duniya ke yi wa kallon wanda ba ya karɓar rashawa.

“A yanzu muna amfana daga kyawawan manufofin Shugaban Ƙasa ba don komai ba sai don duniya ta san cewa wannan wani shugaba ne da ba ya ta’ammali da rashawa- shugaba mai gaskiya da mutunci.

“A halin yanzu, ‘yan Najeriya sun fara amfana da haka”, in ji shi.

Mista Ngelale ya bayyana kyakkyawan fata cewa tafiye-tafiyen Shugaba Buhari za su haifar da ɗa mai ido wajen kafa wata ƙasa mai ƙarfin tattalin arziƙi ta hanyar yarjejeniya tsakanin Najeriya da ƙasashe biyu.

“Tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Tarayyar Rasha da Saudiyya duk ya yi su ne saboda ci gaban ƙasa.

“Ina faɗar haka ne saboda idan ka duba alfanun waɗancan tafiye-tafiye, za ka ga yadda waɗancan tafiye-tafiye suka ƙara wa tattali arziƙin ƙasarmu kima.

“A keɓance, mun yi matuƙar jin daɗi game da tafiya zuwa Rasha saboda yawan tattaunawar da aka yi waɗanda suka haifar da yarjejeniya waɗanda a yanzu an sa hannu tsakanin ƙasashen biyu, wanda duka zai kasance huɗɗa tsakanin gwamnati da gwamnati”, in ji Mista Ngelale.

Hadimin na Shugaban Ƙasa ya ce wasu daga cikin ɓangarorin da kai tsaye za su amfana daga wannan yarjejeniya ta ƙasashen biyu sun haɗa da bunƙasa haƙar ma’adinai, sufuri, haƙar tama da tsaro.

“A ɓangaren haƙar ma’adinai, za a farfaɗo da Kamfanin Sarrafa Ƙarafa na Ajakuta ta hanyar tallafin dala biliyan $1 da Tarayyar Rasha, gwamnatin Najeriya da bankin Afrexim Bank za su raba”, in ji shi.

A ta bakinsa, ta hanyar yin haka, Najeriya za ta iya farfaɗo da Kamfanin Sarrafa Ƙarafan, kuma ta hana shigo da ƙarafa.

“Muna son mayar da ƙasarmu mai arziƙin masana’antu mu ɗauki mutanenmu aiki, mu kuma cire su daga ƙangin talauci.

“Daga ƙarshe sai mu iya samar da ƙarafa da kanmu”, ya ƙara da haka.

Mista Nagelale ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta bada kulawa ta musamman don farfaɗo da Kamfanin Haƙar Tama na Ƙasa, NIOMCO dake Itapke, jihar Kogi.

“Saboda haka, akwai tallafin dala miliyan $400 da aka ware daban don farfaɗo da NIOMCO don mu samu kuzar da za mu riƙa kaiwa Ajakuta don bunƙasa sarrafa ƙarafa”, a kalamansa.

A ta bakin Mista Nagelale, wata yarjejeniya da aka cimma da gwamnatin Rasha za ta sa ƙasar ta Rasha ta ba Najeriya jiragen helikwafta samfurin 12 M1-35, waɗanda za a yi amfani da su wajen shawo kan matsalolin tsaro dake damun ƙasar nan.

“Waɗannan makamai ne masu nauyin gaske, helikwaftoci masu sauri sosai waɗanda za su kawo bambanci a ɓangaren yaƙi da satar fasaha.

“Za mu samu wasu kayayyakin more rayuwa daga gare su kamar ƙananan kwale-kwalen yaƙi, jiragen ruwa na yaƙi da abubuwan da za su taimaka wa tekunanmu.

“Za mu fara ƙera motoci masu aikin jiragen ƙasa a Najeriya don mu rage cunkoso a tashoshin ruwa, a kuma rage wa hanyoyin motoci wahalhalu” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa Masana Ilimin Tarihin Ƙasa na Najeriya da na Rasha za su yi aiki tare don samar da taswirar da za a yi aiki da ita don bunƙasa ɓangaren haƙar ma’adinai na ƙasar nan”.

“Ana sa ran taswirar da za a yi ɗin ta gano wurare, nauyi da yadda ma’adinan suke don zaburar da kuma jan hankalin masu zuba jari a ɓangaren haƙar ma’adinai, wani abu da zai samar da miliyoyin ayyuka ga jama’a”, ya ƙara da haka.

Hadimin Shugaban Ƙasar ya ce Najeriya da Saudiyya sun amince za su kawo manyan ƙusoshin gwamnati waɗanda za su duba wurare masu daraja da ya kamata a haɗa kai a ɓangaren man fetur da iskar gas na tattalin arziƙin Najeriya.

Ya ce za a kafa Hukumar Kula da Alaƙa Tsakanin Najeriya da Saudiyya don ciyar wannan buƙata.

Kamfanin Man Fetur na Saudiyya, Aramco (kamfani mafi girma a hada-hadar man fetur da iskar) yana so ya taimaka wa Najeriya wajen farfaɗo da matatun man fetur, gina fayif-fayif, gina asibitoci masu matakin ƙwarewa a duniya don amfanin ‘yan Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan